✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Qatar za ta fara ba wa Jamus iskar gas

Jamus za ta fara sayen ton Jamus iskar gas da yawansa ya kai tan miliyan biyu daga kasar Qatar sakamakon yankewarsa daga Rasha.

Qatar za ta fara sayar wa Jamus iskar gas da yawansa ya kai tan miliyan biyu sakamakon yankewar iskar daga Rasha.

Jamus ta kulla yarjejeniyar samar mata da iskar gas din ne da Qatar na tsawon shekara 15.

Hakan ya biyo bayan tashin hankalin da Jamus ta shiga saboda rashin samun iskar gas daga Rasha tun cikin watan Agusta a dalilin yakin da Rasha ke yi da Ukraine.

Cikin sharuddan yarjejeniyar, kamfanin gas na gwamnatin Jamus, Conocophilips, wanda ke da jari a mahakar gas na Qatar da ke kan teku, ya yi tarayya da kasar Iran.

A karkashin yarjejeniyar, Qatar za ta rika samar da makamashin ne ta hanyar wata tasha da za a gina a Brunsbuettel

Kasashen turai sun shiga matsalar iskar gas da suke bukata don dumama gidaje da samar da lantarki da kuma motsa injinan masana’antu, bayan Rasha ta sayar musu da gas a dalilin yakinta da Ukraine.

Hakan ya sa farashi ya yi tashin gwauron zabi da ya jefa ’yan kasar cikin tashin hankali.