✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Qausain TV ta kulla alakar aiki da tashar France24

Tashar Talabijin ta kasar Faransa, France 24, ta kulla alakar aiki da Qausain TV da ke nan Najeriya.

Tashar Talabijin ta kasar Faransa, France 24, ta kulla alakar aiki da Qausain TV da ke nan Najeriya.

Shugaban Qausain TV, Malam Nasir Musa Idris (Albani Agege) ya bayyana cewa hakan wani matsayi ne na habbaka daraja da martabar harshen hausa a duniya.

“Lallai alakar zumunci mai karfi ta kullu tsakanin Qausain TV da France24 kuma hadaka ce mai matukar alfanu da za ta zama gadar sadar da Hausawan duniya, domin kara sanin abubuwan da ke faruwa a duniya a saukake,” in ji shi, jim kadan bayan amsa gayyatar da France24 ta yi masa.

Nasir Albani, wanda ke kammala shirye-shiryen fara aikin, ya ce, “A halin yanzu ina kasar Faransa, bayan da muka samu gayyata zuwa birnin Paris inda babban gidan talabijin na France 24 ya sanya ni cikin wadanda za su rika alaka da su a duniya.”

Qausain TV  tashar Talabijin ce da ta yi fice a Najeriya wajen yada shirye-shirye a cikin harsunan Hausa, Turanci da kuma Larabci.