✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ra’ayi: Soshiyal Midiya a Arewa: Aisha Buhari da Aminu Adamu, daga Aliyu Tilde 

Ya zama wajibi in yi rubutun nan saboda abin da na yi karo da shi a awa 24 da suka wuce game da soshiyal midiya…

Ya zama wajibi in yi rubutun nan saboda abin da na yi karo da shi a awa 24 da suka wuce game da soshiyal midiya a Arewacin Najeriya. Abubuwan guda uku ne amma zan bar su a biyu.

1. Aisha Buhari da Aminu Adamu
2. Sanata Ibrahim Musa da Shafi’u Aliyu

Zan yi magana a kan na farko. Na biyu din sai gobe.

Aisha Buhari

Mai girma First Lady, Aisha Buhari, kanwata ce, ban da haka kuma Allah ya hada jininmu sosai. Kuma ina matukar kaunarta. Gaskiya ke nan. Don haka kar a ga laifina in na dau zafi ganin wani ya ci mata mutunci. Ba zan boye muku ba.

Akwai dalibin da ya ci mutuncinta, sunansa Aminu Adamu, dalibi ne a FUDutse a watannin baya. Danmu ne daga Azare. Ya rubuta a shafin Twittter ya ce, “Mama ta ci kudin talakawa ta koshi.” Ga duk mai jin Hausa ya san abin da yake nufi. Ma’ana Aisha ta yi kiba don ta ci kudin al’umma, watau sata. Fakad. Mai son lauyewa sai ya lauye. Amma mu gaskiya za mu fada.

Gaskiya wannan ba da’a ba ne kwata-kwata. Kuma duk uba zai yi wa dansa fada idan ya ga ya rubuta wannan. Aibata mutum da halittarsa kuma ka kara da kazafi bai dace a ce tarbiyyar da yaranmu za su dauka ba ne. Na tabbata Malam Adamu Mohammed, mahaifin Aminu, bai taba yi wa wani shugabansa haka ba. Amma ga dansa ya yi. A ina wannan dan namu, yana dalibi, ya tsinci wannan gubar har ya sha ta kai masa karo?

A soshiyal midiya. Wannan dandali ya ba da dama kowa ya ce komi game da kowa, ko karya ko gaskiya, ba tare da tacewar kwararru na aikin jarida ko taka-tsantsan da tarbiyya ta addini ke bukata ba. Don haka muka gani wasu suna yi a wasu sassa na Najeriya ko a kasashen waje, alhali al’ummarmu da tarbiyyarmu ba ta gaji haka ba. Wannan kuskure ne.

Eh. An gaji a yi shagube kamar yanda Sa’adu Zungur ya yi a 1950s. An gaji a yi suka bisa manufa kamar yanda Malam Aminu Kano ya yi a 1940-60s kuma kamar yanda aka ci gaba da yi zuwa yau, da hujjoji bayyanannu ko da kuwa za a kira suna. Amma a kama sunan mutum, a keta masa mutunci, ta hanyar zagin halittarsa da kazafi, in dai ba bisa kuskure ba, wallahi bai kamata ba kuma ba mahaluki mai hankali da zai kare haka balle kuma daga wajen dalibi wanda ya kamata ya tarbiyyantu da biyayya. Ina shi ina matsayin Aisha? Haba jama’a.

Kuma kiba ga mata (har mu maza) shekaru ke kawo shi. Kowa ya sani. Matanmu a karkara ma suna teba idan shekarun sun zo. Ba sa so. Kuma bai kamata a siffanta su da haka ba. Ita halitta yin Allah ne. In ka bace ta, ka baci yin Allah ne. Don haka Hadisi ya zo Ma’aiki (S.A.W) ya yi hani da haka ko da a bayan mutum ne balle kuma a bainar jama’a da kafa irin ta Twitter.

Haka kuma zancen satar kudi—ko abinda Aminu ya kira cin kudin talakawa. Idan aka ce ya kawo inda Aisha ta dauki kudin da ta sata ta ci har ya sa ta kiba ba zai iya kawowa ba kai tsaye, sai dai tsammani. Da a umumance (generally) ya fada, kila da ba wanda ya damu. Amma kama suna kai tsaye, dole zai jawo hankali da bata suna.

Wasu za su ce ai ana yi wa shugaban kasa bai ce komi ba. Ko Jonathan da matarsa. Haka ne. Amma za ka yi wa Abacha ko Babangida ko Murtala? Kai ko a kasuwa ne, in ka zagi wani sai ya kyale, wani kuwa casa ka zai yi. Sai ka ce hujjarka ita ce ai ka zagi wani bai ce komi ba, me ya sa shi wannan zai daka ka? Don haka, fadakarwa mu bar wannan sabuwar tabi’a kawai shi ya fi alheri.

Hadari

Irin wadannan abubuwa suna da matukar hadari ga masu yinsa. Sau da yawa idan aka gamu da marar imani ya kan kai ga kisa ta hanyar sace mutum a batar da shi bat. Kuma a rasa yanda aka yi. Ko sawu ba za a gani ba. Duk wanda yake Gomnati zai iya sa a yi wannan, sai dai a yi shara’a a lahira.

Masu sauran imani ne suke sa a labatar da mutum ta hanyar horo ko su je kotu don neman hakkinsu. To Wallahi idan d’ana ya yi wa wani babba abinda ba daidai ba gara ya sa a hora shi, kuma ya gaya mun nima zan kawo dauki wajen casa shi, a yi ta Yarbawa idan suna ladabtar da yaro.

Amma banda zuwa kotu neman hakki don diyyar da za a tambaya ba ni da ita ko zan tara dukiyata ne kaf. Yanzu kaddara Aisha ta je kotu ta nemi diyya don bata suna, yaro kuma ya kasa kare kansa, aka nemi biliyoyi, to mu iyaye abokai Malam Adamu ina za mu fito da kudin in ba zare ido ba? 😳 Karyewar arziki ya zo. Don haka gara yaro ya ji a jikinsa. A bani abina mu koma gida ya sha farsa da ruwan zafi. Gobe ko an ce ya yi, ba zai yi ba.

Roko

Na ji dadin da Aisha duk da ikon da take da shi ba ta zabi hallaka Aminu ba. An ce, wai, ta sa an dauko shi an ladabtar da shi sannan aka tsare shi.

Idan haka ne, ba abinda za mu ce sai godiya. Mu iyayen Aminu Mun gode. Mun gode. Wannan zai zama izina ga y’ay’anmu. Zai sa su tuna da tarbiyyar yankinsu da addininsu. Su tuna cewa ba kara zube suke ba. Suna da asali mai daraja da addini maigirma da zai hana su yin ba daidai ba.

Na jima ban ga Aisha ba. Da ina da hanyar ganinta da yau din nan zan je wajenta, in fadi, in nema wa Aminu da mu iyayensa afuwa. Na tabbata, Aisha yar girma ce. Daga gidan girma take. Ta san darajar iyaye. Ta san girman zumunci da kauna. Tabbas, don zumunci da girmamawa da kauna, za ta ban Aminu mu dawo gida.

To amma duk da ba ni da halin ganinta yanzu, ina fata wannan rubutu nawa zai isa gunta. Ta dauka Aminu danta ne, baban Aminu dan uwanta ne. Ta yafe. Ta sa a kira shi, ta masa fada, sannan ta ba da dama ya dawo gida. Useni. Useni!

Wannan shi ne abin da dattijo zai yi a matsayinsa na uba. Ita kuma a matsayinta na shugabarmu yafiya shi ya kamace ta bayan ladabtarwa. Duk wani batu da zai ruruta maganar ba namu ba ne kuma zuga ne kawai na makwangwara.

Ina fata sakona ya isa wajen Aisha. Idan ta ce in zo ta danka mun shi, take zan garzayo in karbe shi in kai shi Azare mu taru mu ja masa kunne.

Madalla. Madalla.

Dr. Aliyu U. Tilde
27 Nuwamba, 2022