✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Raba mutum miliyan 100 da talauci zuwa 2025 abu ne mai yiwuwa —MDD

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce fitar da mutum miliyan 100 a fadin duniya daga kangin talauci ya zuwa 2025 abu ne mai yiwuwa. MDD…

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce fitar da mutum miliyan 100 a fadin duniya daga kangin talauci ya zuwa 2025 abu ne mai yiwuwa.

MDD ta ce duk da barazanar koma-bayan tattalin arziki da ake fuskanta, abu ne da zai yiwu a raba mutum miliyan 100 da talauci nan da shekarar 2025.

Sakamakon binciken da MDD ta fitar kan taulaci a ranar Litinin, ya nuna za a iya rage talaucin da ake fama da shi, kuma samar da sabbin dabaru a fagen yaki da talaucin zai taimaka wa gwamnatici wajen cimma wannan kuduri.

Majalisar ta fitar da sakamakon binciken nata ne albarkacin Ranar Yaki da Talauci ta Duniya, wadda akan yi ran 17 ga Oktoba na kowace shekara.

Ta kara da cewa, domin cimma nasara a wannan yakin, tilas shugabanni da kasashe su mike tare da daukar ingantattun matakan dakile abubuwan da ke haddasa talauci a cikin al’umma.