✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rabin masu yin girki da gas sun koma amfani da itace da gawayi

Kullum farashin gas din girki kara karuwa yake yi.

Akalla mutum biyar cikin kowadanne mutum 10 masu amfani da gas domin girki sun daina amfani da shi, sun koma amfani da itace da kuma gawayi.

Tun lokacin da iskar gas din ta yi tashin gwauron zabo, yawancin mutane, musamman masu karamin karfi suka koma girki da ta itace da gawayi.

Shugaban dillalan iskar gas na kasa, Michael Umudu, ne ya bayyana haka a lokacin da ya zanta da manema labarai a birnin Legas.

Ya koka game da yadda farashin gas din girki yake kara tashi a kowane lokaci inda ya ce su kansu ba su jin dadin yadda farashi ke kara hauhawa.

Ya kara da cewa yanzu ana sayar da kilogirma 12.5 har Naira 9,000 alhali a baya-bayan nan bai wuce N3,800 ba, lamarin da ya ce ba karamin koma baya ya kawo ga tattalin arzikin kasa ba.

An dai alakanta tsadar iskar gas din da hauhawar farashin kaya a kasuwan duniya da kuma karancin samun canjin Dala.