✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Rakumin Dawa: Dabbar da ke barci a tsaye

Rakumar dawa na dauka da dawainiyar ciki na tsawon wata 15 kafin ta haihuwa.

Rakumin Dawa na daga cikin dabbobin da jikinsu ke da kwalliya da kuma daukar hankali a doron kasa.

Masana sun ce nau’ukan rakumin dawa hudu ake da su a duk duniya.

A halin da ake ciki, an daina samun rakumin dawa a wasu kasashen Afirka akalla bakwai.

Kamar dai zanen yatsun mutane, masana sun ce bai yiwuwa a samu rakuman dawa biyu masu zanen jiki iri daya.

Tsayin harshensu yakan kai tsawon santimita 45 zuwa 50.

Da kaho ake haihuwar jariran rakumin dawa. Sai dai kahonnin ba su da kwari ta yadda ba za su cutar da uwar ba a lokacin haihuwa.

Ita ce dabba mafi tsayi a duniya. Kafafunta kadai sun fi mutum tsayi.

Ita ce dabbar da galibi take rayuwa a tsaye, ta huta a tsaye, har barci takan yi a tsaye haka ma haihuwa, sannan dan ya mike da kafafunsa bayan kimanin sa’a daya.

Rakumar dawa na daukar ciki da dawainiyarsa har tsawon wata 15.

A wasu yankunan, galibin ‘ya’yansu ba su tsallake shekararsu ta farko saboda barazanar muggan dabbobin dawa.

A tsaye kuwa, wannan dabbar ba ta iya lankwasa wuyanta su taba kasa da kansu, wannan ya sa idan sun tafi shan ruwa dole sai sun ware kafafuwansu kafin su iya dukawa su sha.

Binciken masana ya nuna ba kullum rakuman dawa ke shan ruwa ba, yakan dauke su kwanaki kafin su sha ruwa ko da kuwa akwai ruwa a wadace kusa da su.

A kimiyyance, nauyin zuciyar rakuman dawa ya kai kilogram 11. Sannan zuciyarsu na iya bugawa sau 40 zuwa 90 a cikin minti daya, inji masana.

Duk da dai babu wani takamaiman sakamakon bincike kan haka, amma ana zaton rakumin dawa zai iya rayuwa na tsawon shekara 25 zuwa sama da haka.

Dabbobi ne masu cin ganye sosai hadi da ‘ya’yan itatuwa da sauransu. Ba su cika cin ciyawa ba.

Bincike ya nuna a halin yanzu, wannan dabbar ba ta da yawa kuma a fadin duniya, tuni aka daina ganinta a wasu kasashen Afirka da kewaye. Hakan kuwa ya faru ne sakamakon sauyin yanayi, barazanar mafarauta, bunkasa da yaduwa mutane da sauransu.