✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: A wanne hali Musulman Ukraine suke azumi a yanayin yaki?

Sai dai Musulman Ukraine sun ce azumin bana ya zo musu cikin mawuyacin hali saboda yaki

A watan Ramadan, Musulmai a duk fadin duniya kan shafe tsawon watan suna azumi, babu ci babu sha tun daga fitowar rana har zuwa faduwarta.

Sai dai a Ukraine, sabanin a sauran kasashen Turai da dama, a bana azumin ya zo yayin da kasar ke tsaka da fuskantar yakin da ya raba miliyoyin mutane da muhallansu.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, mako biyar bayan Rasha ta mamaye kasar ta Ukraine, kusan mutum miliyan 10 ne suka rasa muhallansu, ciki har da wasu miliyan hudun da suka fice suka bar kasar.

Musulmai da dama dai da suka bar kasar, da ma wadanda suka zauna a ciki na bukatar tallafin gaggawa saboda mawuyacin halin da suka fada.

A kasar Ukraine dai, adadin Musulmai bai wuce kaso daya cikin 100 ba, yayin da mabiya Kiristanci ke da kaso mafi rinjaye.

Gidan talabijin na Aljazeera ya rawaito cewa akwai Musulmai ’yan asalin kasar Turkiyya sama da 20,000, musamman a yankin Crimea.

Niyara Mamutova, Shugabar Kungiyoyin Musulman Ukraine ta ce yanayin yakin ya canza kusan komai na rayuwarsu.

Niyara dai ta rasa muhallinta da ke Kudu maso Gabashin lardin Zaporizhzhia.

Ta ce a ranar azumin farko, ta yi yunkurin shirya bude-baki ga wasu iyalai da suke zaune tare a cibiyar Musulunci ta Chernivtsi.

Sai dai ta ce yanayin yakin ya sa azumin na bana ya zo musu da tarin kalubale kusan ta kowace fuska, sakamakon karar bama-bamai da dokokin kullen da ake kakaba wa.

Kazalika, ta yi korafin cewa akwai dokokin hana zirga-zirga da yamma, lokacin da iyalai kan taru don yin bude-baki.

Ita ma wata matar daya daga cikin limaman kasar, Mamutova, ta ce, “Dole mu shirya yin iya kokarinmu wajen neman gafarar Allah, yin addu’a ga ’yan uwanmu da ma kasarmu ta Ukraine a watan azumin nan.”