✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: Kungiya ta tallafa wa masu karamin karfi 550 da kayan abinci a Kano

Wadanda suka amfana da tallafin dai yawancinsu magidanta ne maza da mata.

Wata kungiya mai rajin tallafawa masu karamin karfi a jihar Kano mai suna NUSAID a ranar Lahadi ta tallafawa mata da magidanta 550 da kayan abinci a jihar.

Kungiyar, tare da hadin gwiwar Zauren Malaman Kano dai ta rabawa mutanen kayan tallafin ne da suka hada da shinkafa da taliya da man girki da sukari da kuma kudi domin su yi amfani da su a watan Azumin Ramadan.

Da yake jawabi yayin rabon tallafin, jami’in kungiyar ta NUSAID, Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa ya ce kungiyar ta zakulo mabukatan ne daga sassa daban-daban na jihar.

Wasu daga cikin mutanen da suka rabauta da tallafin
Wasu daga cikin mutanen da suka rabauta da tallafin

Ya ce, “An bi masallati da majalisun karatu ne aka zakulo mabukata sannan aka tattara sunayensu kafin a tantance su.

“Mun sa sharadin dole sai mun san ko dai wacce aka mutu aka bar wa marayu ce ko kuma magidancin da wata larura ta sa ba ya iya fita neman abincinsa kafin ya iya cin gajiyar tallafin.

“Yau mun ba kimanin mutum 550 tallafin shinkafa da taliya da man girki da gishiri da magi da sukari da kuma kudin mota,” inji shi.

Daga nan sai ya yi kira ga sauran masu hannu da shuni da su rika taimakawa masu karamin karfi a cikin al’umma, ba kawai a watan Azumin ba.

Ya ce tun kafuwar kungiyar a shekarar 2016, ta taka muhimmiyar rawa wajen bayar da tallafi ga jama’a da dama, ciki har da ’yan gudun hijira a jihar Borno.

Shima da yake tsokaci yayin bikin, Limamin Masallacin Dantata dake unguwar Kofar Ruwa a Kano kuma wakili a Kwamitin Hadin Kan Limamai na kungiyar, Sheik Nura Arzai ya jaddada muhimmancin taimakon masu karamin karfi a cikin al’umma.

A cewarsa, “Manzon Allah S.A.W ya ce Allah yana cikin taimakon bawa matukar bawan yana cikin taimakon dan uwansa.

“Saboda haka duk wanda yake da wata bukata a wurin Allah to ta hanyar taimakon talakawa ya kamata ya nemi taimakon Allah, musamman ta hanyar ciyarwa,” inji shi.

Ya ce matukar masu hannu da shuni za su ci gaba da taimakawa masu karamin karfi, Allah zai ci gaba da yalwata musu tare da share musu hawayensu.

Aminiya ta rawaito cewa wadanda suka amfana da tallafin wadanda yawancinsu magidanta ne maza da mata sun rabauta da karamin buhun shinkafa, jarkar man girki daya da kwano sukari da taliya da dai sauransu.