✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: ‘Mu dage da addu’o’in magance rashin tsaro da COVID-19’ 

Tijjani Tumsah, ya bukaci Musulmi da su rubanya ayyukan alheri a wannan Ramadan.

Tsohon Sakataren Riko na Jam’iyyar APC na Kasa, Tijjani Tumsah, ya yi kira ga al’ummar Musulmi su yi amfani da watan Ramadan wurin yin addu’o’in kawo karshen matsalar rashin tsaro da ta addabi Najeriya.  

Ya kuma bukaci Musulmin Najeriya da su daga da addu’o’i don ganin an kawo karshen cutar COVID-19.

A cewarsa, wajibi ne Musulmi su zama cikin shiri kan abubuwan da suke faruwa a fadin duniya na tabarbarewar sha’anin tsaro, don haka ya bukace su da su kai rahoton duk wani abu da ba su gane masa ba ga jami’an tsaro

Tumsah, ya bukaci daukacin ’yan Najeriya da su roka wa Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari lafiya da fatan ya dawo gida lafiya daga ganin Likita da ya je asar Ingila.

A karshe, ya yi kira ga daukacin Musulmi da su rubanya ayyukansu na alheri a wannan wata mai alfarma.