✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: Mu koma mu tare a Fadar Allah — Atiku

Mu ribaci wannan lokaci wajen kai wa Allah koken matsalolin da suka addabi kasar nan.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi kiran al’ummar Musulmi da su koma su tare a Fadar Allah wajen kadaita shi da bauta a wannan wata na Azumin Ramadana.

Atiku ya yi kiran ne cikin wani sakon taya dukkan Musulmin duniya murnar shigowar mafi falalar wata, wanda ya wallafa ranar Talata a shafinsa na Twitter.

Waziri Adamawa, ya kuma ja hankalin Musulmin Najeriya kan muhimmancin amfani da wannan lokaci wajen kai wa Allah koken matsalolin da suka addabi kasar domin samun sauki.

A cikin sakon nasa, Atiku ya fadakar da Musulmin kasar kan ribatar falalar da wannan wata ya kunsa ta hanyar ingantu ayyuka wajen taimakon juna da bayar da sadaka musamman ga mabukata.

“Wannan lokaci ne da ya kamata mu sake waiwaye kan yadda za mu inganta rayuwar da mutunta juna ta hanyar bayar da sadaka musamman ga wadanda ke da tsananin bukatar taimako.

“Mu rungumi zaman lafiya sannan mu dage wajen gudanar da kyawawan ayyuka domin cimma daidaikun burikanmu da ma na sauran al’umma.”