✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: Abin da ya sa Najeriya ba ta bin lissafin Saudiyya

Dalilin bambancin ganin watan Saudiyya da Najeriya

Mas’alar ganin wata a Najeriya batu ne da ya jima yana janyo ce-ce-ku-ce kusan a kowace shekara, musamman idan watan Azumin Ramadan ya gabato ko na sallah.

Hakan ya jima yana jefa rudani a zukatan Musulman Najeriya, game da lissafin kwanan watan Musulunci da fi dacewa su yi amfani da shi.

Shi ya sa kusan a kowace shekara suke shan bamban wajen daukar azumin Ramadan ko ajiyewa domin sallar idi da sauransu.

Ko a bara an samu irin wannan matsalar a karshen azumin Ramdan sakamakon sanarwar rashin ganin watan Shawwal da ya sa tilas aka cika azumi 30.

Sai dai wasu da suka yi ikirarin ganin watan sun ki bin umarnin Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar III na a cika azumi 30, inda suka yi sallar idi kafin ta sauran mutane.

Ganin wata: Mene ne abin dogaro?

Yawancin mutane dai na tunanin cewa ya kamata Najeriya ta rika bin ganin watan kasar Saudiyya wajen lissafin kwanan watan Musulunci.

Amma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ce Najeriya ta dogara ne da ganin watan al’ummar Musulmi da aka tabbatar da ganin watansu daga wurare daban-gaban, ba wai lissafin kwanan wata kasa ko kalanda ba.

Yadda abin ya ke

A tattaunawarsa da Aminiya, shahararren malamin nan mai ilimin falaki da ke Kaduna, kuma dan Kwamitin Ganin Wata na Kasa, Shaikh Salihu Muhammad Yakub ya ce Najeriya tana amfani ne da ganin wata ba lissafin Saudiyya ba.

Hakan ne a cewarsa, ya sa kasar Ingila ta tabbatar da cewa Najeriya na daga cikin kasashe hudu a duniya masu amfani da ganin wata ba wai lissafin kalanda ba.

Malamin ya ce hakan ne ma ya sa Kwamitin Ganin Wata na Kasar Ingila ya amince da daina amfani da lissafin Saudiyya ya kuma rungumi na Najeriya.

Bambancin lissafin Saudiyya da Najeriya

Ya ce, “Idan ka bi tarihi, daga shekara bakwai da suka gabata zuwa yanzu, kusan a kowane wata Saudiyya tana gabanmu da kwana daya, har sai an zo watan Sha’aban sai su nasu ya cika 30 sannan mu daidaita a Ramadan.

“Abin da ya jawo haka kuwa shi ne ita (Saudiyya) da lissafin kalanda take amfani, sai an zo Ramadan ne suke jingine ta, su yi amfani da ganin wata.

“Amma mu Najeriya hatta wannan sabon watan da ya kama sai da muka yi amfani da ganinsa kafin mu sanar da kamawar sabo. Ba wai da ka ake yi ba.

“Yawancin masu kawo rudani a harkar za ka ga ba sa bibiyar lissafin ne ko yadda ake sanar da shi, sai watan azumi ya zo; wasu daga cikinsu ma watan na wucewa sukan mantawa da lissafin.

“Saboda haka yawanci rigimarsu ta son zuciya ce ba wai ta ilimi ba,” inji malamin.

Bin Saudiyya ba sharadi ba ne’

Sheik Salihu ya ce la’akari da wannan matsayi, ba wajibi ba ne ga kowace kasa ta yi amfani da lissafin kwanan watan Saudiyya matukar ita kasar da ganin wata take amfani kamar irin na Najeriya.

Hakan, a cewarsa shi ne dalilin da ya sa ake samun bambanci tsakaninta da sauran kasashen duniya.

Lokutan da bai kamata a saba da Saudiyya ba

Game da bambancin lissafin kwanan watan Musulunci da ya shafi ayyukan ibada kamar Hajji da hawan Arfa da mutane daga sassan duniya ke haduwa a wuri guda a kasar Saudiyya su gudanar, malain ya yi karin haske.

Ya ce a duk lokacin da aka samu sabanin lissafi da Saudiyya musamman a lokacin aikin Hajji, to yanke hukunci kan lamarin magana ce ta ilimi wadda sai malamai sun zauna sun tsefe ta kafin su bayar da fatawa.

Ya ce, “Akwai kasashen da tuni suka yanke hukunci a kan cewa a duk lokacin da lissafinsu ya saba da na Saudiyya, to idan aka zo watan Zhul-Hijjah za su ajiye nasu su dauki nata, saboda a can ne ake da Arafat ake  kuma aikin Hajji.

“Kazalika, akwai kuma wadanda suka bayar da fatawar cewa ko da an samu irin wannan lamari za su ci gaba da amfani da nasu lissafin.

“Ba wai magana ce ta ra’ayi da ni zan fadi me nake gani ya dace ba, dole sai malaman kasa sun zauna a kungiyance sun ba da fatawa tukunna.

“Ko mu nan a Najeriya, kasashen Yarabawa sun yanke shawarar amfani da fatawar jingine lissafinsu su dauki na Saudiyya a yanayin lokacin aikin Hajji, mu ne a Arewa har yanzu muka kasa cimma matsaya.

“Amma a ragowar watanni kowace kasa za ta iya amfani da lissafin ganin watanta, ko da kuwa ya saba da na Saudiyya,” inji malamin.