✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: Zakzaky ya raba kayan abinci ga mabukata daga gidan kurkuku

Sauran Jihohin da suka amfana da rabon sun hada da Sakkwato da Kebbi da Kano da Filato da Nasarawa da kuma jihar Bauchi.

Shugaban Kungiyar Mabiya Shi’a ta Najeriya (IMN), Sheikh Ibraheem Zakzaky ya raba kayan abinci na miliyoyin Nairori ga mabukata albarkacin watan Azumin Ramadan.

Kayan Abincin da aka rarraba sun hada da buhunan Shinkafa da Sukari da Masara da Gero kuma dansa, Muhammad Ibraheem Zakzaky ne ya jagoranci rabawa a madadin mahaifin nasa.

A wata takarda da ya sanya wa hannu, Muhammad Ibraheem Zakzaky ya ce mahaifin nasa ya bayar da umarnin rabon kayan Azumin ne ga mabukata.

Ya ce, “Mahaifina wanda yanzu haka yake tsare a gudan kurkuku, shine ya bayar da umarnjn raba kayan abincin don a tallafawa mabukata a Najeriya a watan Azumin Ramadana mai Albarka.

“An kammala rabon kayan a Zariya dake jihar Kaduna da wasu Kananan Hukumomin dake fadin jihar kuma wannan wani aiki ne da mahaifin nawa ya kwashe kusan shekaru 20 yana yinsa.

“Zai ci gaba da yin haka ko da bayan gwamnatin Buhari ta shude wadda ta kashe dumbin mabiyansa da suka hada ’ya’yansa uku da aka kashe,” inji shi.

Muhammad ya kara da cewa, Malamin na taya daukacin al’umar Musulmi murnar zagayowar watan tare da tabbatar musu da cewa suna cikin addu’o’insa a wannan wata na Azumi.

Bugu da kari, an rarraba kayan abincin a matsugunan ’yan gudun hijira dake jihohin Katsina da Zamfara.

Sauran Jihohin da suka amfana da rabon sun hada da Sakkwato da Kebbi da Kano da Filato da Nasarawa da kuma jihar Bauchi.