✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: Zulum ya ninka wa ma’aikatan wucin gadi a Borno albashinsu sau uku

Karin dai zai shafi ma’aikatan da ke daukar N10,000 a wata

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sanar da rubanya wa ma’aikatan wucin gadi a Jihar albashinsu har sau uku albarkacin watan Ramadan.

Karin dai zai shafi dukkan ma’aikatan wucin gadi da ke daukar albashin N10,000 a wata.

Gwamnan ya sanar da karin ne lokacin da ya jagoranci duba rabon kudi da kayan abinci ga ma’aikatan a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Maiduguri a ranar Litinin.

Ya ce, “Ina alfahari da dukkanku saboda yadda kuke jajircewa a aiki da kuma tabbatar da tsafta da gyaran Gidan Gwamnati.

“Wannan watan Ramadan ne, kuma kamata ya yi duk wata kyautatawa ta fara daga gida, wannan ne ma dalilin da ya sa na yanke shawarar tallafa muku da abinci da wasu ’yan kudade don ku taimaki iyalanku a wannan watan mai albarka,” inji shi.

Gwamnan ya kuma roke su da su yi amfani da watan wajen yin addu’ar dawowar zaman lafiya a a Jihar da ma kasa baki daya.