✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadana: Tsohon Gwamna ya raba kayan abinci na Naira biliyan 1.4 a Zamfara

Mun yi hakan ne don inganta rayuwar al’umma da ta kasance daya daga cikin manufofin jam’iyyar APC.

Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari, ya yi rabon kayayyakin abinci na naira biliyan 1.4 ga Musulmi a matsayin tallafin watan Azumin Ramadana.

Kayayyakin abinci makare a manyan motocin daukan kaya 130 sun hada da na shinkafa 54, motoci 32 na sukari da kuma 44 na masara da gero.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, an yi rabon kayayyakin abincin ne dukkan Kananan Hukumomi 14 na Jihar Zamfara.

Karamar Hukumar Gusau wacce ta kasance babban birnin Jihar, ta samu buhunan shinkafa 2,400, buhu 1,200 na sukari da buhu 600-600 na masara gero.

Kowace Karamar Hukumar daga cikin ragowar 13 na Jihar sun samu buhunan shinkafa 1,200, buhun sukari 600, da kuma buhu dari uku-uku na masara da gero.

Buhunan kayan abinci da aka raba a Zamfara

Wannan tagomashi da tsohon Gwamnan ya yi a ranar Litinin na zuwa ne a daidai lokacin da Musulmi ke shirin fara Azumin watan Ramadana wanda ya kasance daya daga cikin rukunan ibadu na addinin Islama.

Buhunan Sukari da aka rabar

Tsohon gwamnan wanda Sanata Kabiru Marafa ya wakilta yayin rabon kayayyakin, ya ce ya yi hakan ne domin taimaka wa musulmi mabukata da kuma inganta rayuwar al’umma da ta kasance daya daga cikin manufofin jam’iyyarsu ta APC.

Ya yi kira ga al’umma da su ribaci wannan lokaci na Ramadana wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.