✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar 9/11: Shugaban Al-Ka’ida ya fitar da sabon bidiyo

Bayan kusan shekara ana tunanin ya mutu, shugaban kungiyar ya fitar da sabon bidiyo.

Bayan kusan shekara guda ana tunanin Shugaban kungiyar Al-Qaida, Ayman al-Zawahri, ya mutu, sai ga shi ya fita a wani sabon bidiyo kan cika shekara 20 da hare-haren ranar 11 ga watan Satumba, 2001 da aka kai wa Amurka.

Kungiyar SITE, mai binciken kwakwaf, wadda kuma takke sanya ido kan shafin intanet na Al-Qaida, ta ce a ranar Asabar da aka yi bikin ne Al-Qaida ta dora bidiyon al-Zawahri a shafinta, kuma a ciki ya yi magnaa kan ficewar sojojin Amurka daga Afghanistan bayan shekara 20.

An kuma ji shugaban na Al-Qaida yana cewa, “Ba za a taba yahudantar da Birnin Kudus ba”, sannan ya yaba hare-haren kungiyar, ciki har da wanda ta kai wa sojojin Rasha a cikin watan Janairun 2021 a kasar Syria.

SITE ta ce ko da yake al-Zawahri ya yi batu a kan janyewar dakarun Amurka, babu tabbacin cewa a kwanan nan ya yi jawabin nasa, saboda tun a watan Fabrairun 2020 aka sanya hannu kan yarjejeniyar janyewar sojojin na Amurka daga Afghanistan.

A sabon bidiyon dai shugaban na Al-Qaida bai yi magana game kwace mulki da kafa sabuwar gwamnati da Taliban ta yi ba a Afghanistan.

Bai kuma yi magana ba a kan harin ranar 1 ga watan Janairun 2021 da aka kai wa sojojin kasar Rasha a birnin Raqqa na kasar Syria.

Tun a karshen shekarar 2020 da aka fara rade-radin cewa al-Zawahri ya rasu bayan fama ya sha fama da rashin lafiya.

Tun daga lokacin ba a kara jin duriyarsa ba, sai a bidiyon da kungiyar ta fitar a ranar Asabar – daidai lokacin da Amurka ke makokin cikin shekara 20 da harin da aka kai mata da jirage a Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da Hedikwatar Tsaro ta Pentagon.

Amma Daraktan SITE, Rita Katz, ya ce duk da sabon bidiyon mai tsawon minti 61 da sakan 37, tana iya yiwuwa Ayman al-Zawahri “Ya riga ya rasu, in kuma hakan ne, to ya rasu ne a cikin watan Janairun 2021 ko bayan nan”, kamar yadda ya wallafa a Twitter.