✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Abinci Ta Duniya: Ko Najeriya na daga cikin kasashe masu wadatar abinci?

A shekarun baya, Najeriya ba ta san da matsalar karanci ko tsadar abinci ba.

Ranar 16 ga Oktoban kowace shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don bikin ranar da aka kafa Hukumar Abinci da Bunkasa Noma ta Majalisar Dinkin Duniya a 1945.

Tun daga wancan lokaci, yayin zagayowar wannan rana a duk shekara, hukumomi da kungiyoyi masu alaka da harkokin noma da samar da abinci a sassan duniya, kan gabatar da shirye-shirye kan batutuwan da suka shafi samar da abinci domin fadakarwa da kuma wayar da kan al’umma.

Misalan wadannan batutuwa sun hada da; yadda za a samar da isasshen abinci da kawar da yunwa da sauran matsalolin da ke kassara wadatar abinci a tsakanin al’umma da dai sauransu.

Yadda kasa take wadatuwa da abinci

Babban Taro na Duniya da aka gudanar kan batun abinci a 1996, ya yarda cewa ana ayyana kasa a matsayin mai wadatar abinci ne yayin da ya kasance al’ummarta na samun abin da za su ci a wadace, cikin sauki kuma mai gina jiki.

Matsalar yunwa a kasashen Afirka

Sai dai bincike ya nuna a Afirka, kusan kowane mutum daya a cikin hudu na fuskantar rashin samun wadataccen abinci.

Amma tsadar kayan abinci da fari na ci gaba da ta’azzara wa al’umma matsalar karancin abinci a sassan daban-daban.

Mene ne wadatar abinci?

Wadatar abinci na nufin, ya kasance kasa na da isasshen abincin da al’umma za su ci, ya kuma kasance a kan farashin da ba zai gagari talakawan kasar ba.

Najeriya wadda ake yi wa kallon uwa ma-ba-da-mama a tsakanin kasashen Afirka, noma na daga cikin manyan hanyoyin da kasar ke tinkaho da su wajen samun arzikinta.

Duk da irin dimbin arzikin da Najeriya ke da shi, masana tattalin arziki na ra’ayin kasar ba ta samu irin ci gaban da ya kamata ba, don kuwa kimanin kashi 70 na al’ummar kasar na fama da talauci.

Najeriya ce ta 40 a kasashe masu fama da yunwa

Haka nan, a 2012, kididdigar cibiyar tantance yunwa a kasashe ta duniya ta nuna Najeriya ce ta 40 daga cikin kasashen duniya 79 da suka fi fama da yunwa. Sannan mazauna karkara a sassan kasar su ne matsalar ta fi addaba.

Galibi, babbar matsalar ‘yan karkara a Najeriya wanda kuma su ne manoman na asali, ita ce rashin fasahar zamani wajen adanawa da kuma tattalin amfanin da suka girba, wannan matsalar da kuma talaucin da suke fama da ita su suka hade suka zame musu babban kalubalen da suke fuskanta.

Najeriya ta ciri tuta noman Rogo da Doya

A 2012, Asusun Bunkasa Harkokin Noma (IFAD), ya ayyana Najeriya a matsayin ta farko a duk duniya a fagen noman doya da rogo, duk da haka wannan bai hana kasar fama da yunwa ba.

Ga kuma dogaro da takan yi wajen shigo da abinci daga ketare duk da arzikinta.

Najeriya tana da kashi 75 na kasar noma

Allah Ya albarkaci Najeriya da kasar noma, domin kashi 75 cikin 100 na kasar wadda za a iya nomawa ce, amma sai ya zamana kashi 40 kacal ake nomawa.

Sannan galibin manoman masu karamin karfi ne wadanda iya abin da za su ci suke nomawa sai kuma wani kaso na amfanin da sukan sayar don samun rufin asiri.

Kalubalen da manoman karkara ke fuskanta a Najeriya

Duk dai su ne mafi yawan manoman da kan samar da abinci a kasa, mazauna karkara na fuskantar kalubale masu yawa wanda ke tsananta talaucin da suke fama da ita.

Misali, babu hanyoyi masu inganci wadanda za ba su damar jigilar amfanin gonar da suka noma zuwa kasuwanni da sauran sassa cikin sauki, ga rashin kayan aiki irin na zamani wanda zai saukaka musu wajen aikin gona da kuma fadada noman da suke yi.

A da Noma ita ce abar tinkaho a Najeriya

Abin tambaya a nan shi ne, a shekarun baya, Najeriya ba ta san da matsalar karanci ko tsadar abinci ba, me ya sa daga baya kasar ta tsinci kanta cikin wannan hali?

Amsar ita ce, kafin wannan lokaci harkar noma ita ce abar da Najeriya ke tinkaho da ita. Da noma kasar ke ci da sha da sauran bukatunta.

A wancan lokaci, Arewa ta shahara a fagen noman gyada, yayin da Kudancin kasar ya shahara wajen samar da koko da roba da kwakwar manja da sauransu, wanda da wadannan amfani akan ci na ci a kuma sayar da na saidawa a gida da ketare.

Abin da ya janyo wa Najeriya koma baya a harkar Noma

Haka dai lamarin ya ci gaba har zuwa lokacin da aka gano arzikin mai a Kudancin kasar, inda maimakon a hada noma da mai a ci gaba da rike kasa da su, sai aka saki noma aka rungumi harkar mai saboda ganin ta fi kawo makudan kudi cikin kankanin lokaci.

Wannan shi ne silar matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yau dangane da abin da ya shafi wadata kasa da abinci.

Matsalolin da ke haifar da rashin wadatar abinci a kasa —Kwararru

Kwararru sun ce, matsalar da ke haifar da rashin wadatar abinci a kasa yawa gare su, ciki har da: rashin tsaro, rashawa, rashin adalci daga bangaren masu jagorancin harkokin al’umma.

Sauran sun hada da rashin bai wa fannin noma muhimmanci, rashin samar da tsare-tsare masu inganci, rashin jituwa tsakanin al’ummomi, rashin amfani da fasahar zamani da sauransu.

Ya kamata gwamnati ta zage dantse

Idan aka duba, da dama daga cikin matsalolin da aka lissafo a sama Najeriya na fama da su, kuma har sai an dukufa an dauki matakin kawar da su sannan kasar za ta kasance mai watadar abincin da al’ummarta za ta kasance cikin walwala.

Abinci dai shi ne rayuwa, idan babu abinci rayuwa ba za ta yiwu ba. Don haka, akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta kara himma wajen wadata kasar da abinci ta hanyar daukar kwararan matakai tare da sanya ido sosai wajen tabbatar da ana aiwatar da matakan kamar yadda aka tsara.