✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Dimokuradiyya: Buhari zai yi wa ’yan Najeriya jawabi ranar Lahadi

Buhari zai yi jawabi albarkacin Ranar Dimokuradiyya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi wa ’yan Najeriya jawabi ranar Lahadi, 12 ga watan Yunin 2022.

Jawabin, wanda zai kasance na Bikin Ranar Dimokuradiyya ne za a watsa shi da misalin karfe bakwai na safe.

Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Shehu ya bukaci dukkan kafafen watsa labaran gwamnati na rediyo da talabijin su yi aika kafada-da-kafada da tashoshin FRCN da NTA domin watsa jawabin kai tsaye.