✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Dimokuradiyya: Gwamnati ta ba da hutun yini guda

Mu tabbatar cewa Najeriya ta ci gaba da zama kasa dunkulalliya, mai hadin kai kuma mai tsaro da zaman lafiya.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 13 ga Yunin 2022 a matsayin ranar hutun gama-gari albarkacin Bikin Ranar Dimokuradiyya.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Alhamis.

Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen taya ‘yan Najeriya murna dangane da bikin wannan rana, tare da yin kira ga daukacin ‘yan kasa da a ci gaba da mara wa gwamnatin bayan wajen ganin ta inganta ayyukanta a dukkanin fannoni.

Ya ce, “Yayin da muke bikin Ranar Dimokuradiyya, ya kamata mu waiwaya mu dubi kokarin magabatanmu sannan mu tabbatar da Najeriya ta ci gaba da zama kasa dunkulalliya, mai hadin kai kuma mai tsaro da zaman lafiya.”

Ya ci gaba da cewa, “Duba da kalubalen da muke fuskanta yau a Najeriya, kada hakan ya sa mu rarraba, face mu so juna da gaskiya ta yadda za mu fahimci juna da girmamawa sannan mu zauna tare cikin lumana.”

Kazalika, Aregbesola ya shawarci ‘yan Najeriya da su yi amfani da sabuwar manhajar nan ta tsaro da aka kaddamar kwanan nan, wato Nigeria Internal Security and Public Safety Alert System (N-Alert) domin yaki da matsalar tsaro da sauransu.

Ya kuma ba da tabbacin cewa Najeriya za ta ci gaba da bunkasa duba da irin kokarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi wajen daidaita lamurran kasa.

A Najeriya, an rinka gudanar da bikin wannan rana ne tun daga shekarar 2002, haka kuma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara wa wannan rana karfi a shekarar 2018 bayan da ya sauya Ranar Dimokuradiyyar daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa ranar 12 ga watan Yuni.

Bikin na bana ya kama ne a ranar Lahadi, wanda ya sa aka ayyana Litinin a matsayin ranar hutu.