✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Juma’a kotu za ta yanke hukunci kan karar da ASUU ta daukaka

ASUU na bukatar a jingine umarnin da kotun ma'aikata ta ba ta na janye yajin aiki

A ranar Juma’a Kotun Daukaka Kara za ta yanke hukuncin kan bukatar da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) na jingine umarnin da Kotun Ma’aikata ta ba ta na ta janye yajin aikin da take yi.

Ganin ba ta gamsu da umarnin da Kotun Ma’aikatan ta bayar kan malaman jami’o’i su koma bakin aiki ba, ya sanya ASUU garzayawa Kotun Daukaka Kara don ci gaba da neman bukatunta a wajen gwamnati.

Lauyan ASUU, Femi Falana (SAN), ya ce daidai ne daukaka kara da kungiyar ta yi kan umarnin kotun, saboda a cewarsa, umarnin ya saba mata.

Falana ya bukaci Kotun Daukaka Karar karkashin Mai Shari’a Hamma Barka, da ta janyen adawar gwamnatin ga bukatar daukaka karar da ASUU ta shigar kotu.

Ya kara da cewa abu ne mai hatsari hana wanda yake karewa (ASUU) daukaka kara zuwa gaba.