✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Juma’a Kotun Koli za ta yanke hukunci kan rikicin APC a Kano

Duk hukuncin da aka yanke dai shi ne zai kasance na karshe

A ranar Juma’a ce Kotun Koli za ta yanke hukunci na karshe kan rikicin shugabancin da ya dabaibaye jam’iyar APC a Jihar Kano.

Idan dai ba a manta ba rikici ya barke a jam’iyyar bayan darewarta gida biyu; tsagin Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje da na G-7 da Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta.

Masu daukaka kara a Kotun Kolin sun hada da Musa Chila da wasu mutane 1,319 sai kuma wadanda ake kara Gwamna Mai Mala Buni, Sanata John Akpanudoehe, da Olayide Adewale Akinremi, da Sanata Abba Aji, sai Dokta Tong Macfoy.

Sauran sun hada da Auwal Abdullahi, da Usman Kaita, da Adebayo Iyaniwura da kuma Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC).

Idan za a iya tunawa dai masu karar wadanda yan amanar G-7 ne, sun samu nasara a kotun farko, kafin daga bisani kotun daukaka kara ta basu ruwa.

Rashin gamsuwa da wannan hukunci ne ya sanya suka garzaya kyotun Kolin domin neman hukunci na karshe.

Sai dai wasu daga cikin korafe-korafen da wadanda ake kara ba su gamsu da su ba kamar yadda suka bayyanawa kotun, shi ne matsalarsu da daliget-daliget da za su jagoranci Babban Taron APC na kasa, da tuni aka gudanar.

Bayan sauraren daukaka karar ranar takwas ga watan Afrilu, kotun bisa jagorancin Mai Shari’a Mary Peter Odili ta dage karar.

Daya daga cikin lauyoyin ya shaida wa wakilinmu cewa kotun ta kira bangarorin biyu inda ta ce ta shirya yanke hukunci a ranar Juma’a.

Tun da dai aka sanya wannan rana yayin da kowanne bangare ke cike da fatan samun nasara a shari’ar.