✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ranar Keke Ta Duniya: Abinda Likitoci da ’yan Najeriya ke cewa kan dawo da sufurin keke

Keke yana taimaka wa jiki sosai musamman zuciya.

Ranar uku ga watan Yunin kowacce shekara Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar sufurin Keke ta Duniya, domin wayar da kan mutane kan muhimmancin amfani da Keken, wanda aka fara gudanar da bikin wannan rana tun a shekara ta 2018 a taronta na 72.

Ana dai wayar da kan mutane kan alfanun da ke tattare da hawansa a matsayin hanyar sufuri, da kuma kara lafiyar jiki, da rage matsalolin gurbatar muhalli da muhalli da yake yi.

A kasashe irinsu Indiya da yankin Asiya, amfani da Keke a sufuri ba sabon abu ne, domin maza da mata na hawa, har ma da gurin wasanni domin tsere.

Ko a nan gida Najeriya ma a jiya Hukumar Kiyaye Hadurra Ta Kasa FRSC ta bakin shugabanta reshen jihar Kogi Stephen Dawulung ya ce Najeriya za ta dawo da sufurin Keke, saboda sauki da hakan ke tattare da shi ga al’ummar da kuma hukumar.

Abin da ’yan Najeriya ke cewa kan dawo da sufurin keke

Hakan ne ya sanya muka tattaro ra’ayin mutane dangane da wannan batu inda wani Sulaiman Isa ya bayyana mana cewa shi a yanzu ma da shi yake zuwa gurin aiki, kuma yana jin dadin haka, domin Keke ba kamar sauran abubuwan hawa ba ne, ba ya bukatar fetir, ko gas, ko wani sinadari kafin yayi aiki.

Haka zalika ya ce ko matsala ya samu, kayan gyaransa na da matukar arha, da saukin samu ba kamar sauran ababan hawa ba.

“Ko a gurin aiki ana tsokanata ana min dariya, amma ko a jikina, domin ina ji suna kukan rashin kudin mota ko tsadarsa, ni kuwa ba ruwana, sannan ko lalacewa yayi sau da dama ni nake gyara abuna saboda shi ba wasu injina ne a cikinsa ba, ga sauri, ga kuma zan daga shi da hannuna idan na tarar da cinkoso a titi”, in ji shi.

To sai dai wata Safara’u Khamis cewa tayi wannan doka ko za ta yi aiki ba dai a kan kowa ba idan aka zo arewacin Najeriya, kuma a jihohi irinsu Kano, kasancewar zai dauki lokaci kafin al’ummar jihar su amince mata su hau Keke, saboda ya sabawa al’adarsu”.

Alfanu da shawara kan kudirin daga Likitoci

A hannu guda, wani Likita da ke Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kudun Jihar Jigawa mai suna Dokta Khalifa Usman Abdullahi, ya ce keke na taimaka wa jiki sosai musamman zuciya, magudanan jini, da kuma huhu.

Ya ce dogon numfashin da mai tuka Keke ke yi, da gumi da yake fitarwa, da kuma dan zafin da jikinsa ke dauka yayin tuka shi, na taimakawa wajen rage teba.

Dokta Khalifa ya kuma ce yana rage matsalolin ciwon gabobi, ciwon zuciya, mutuwar barin jiki, ciwon suga. Haka kuma a bangaren halitta Dokta ya ce yana kara karfin tsoka da kashi, da rage kitsen jiki da kuma cututtukan damuwa da bacin rai.

To sai dai Likitan ya ce hakan ba wai yana nufin mutum ya wuni yana jan Keke ba, minti 20 a rana ya wadatar, sai dai ya ce yinsa akai-akai taimakwa wajen kona sinadaran da jiki ba ya bukata.

Ya ce hawa Keke ba iya na matasa ba ne ko maza, ko kuma masu kiba, ko larura, kowa zai iya hawa ya yi masa amfanin da aka zayyana, domin yana rage bayyanar tsufa da wuri ga wanda shekarunsa suka ja.

Haka kuma ya ja hankali gwamnati kan samar da wadataccen hasken fitilun titi, da kuma fitar da hannun masu hawansa kamar dai yadda sauran kasashen da ya yawaita ke yi, domin gujewa hadurra kafin dawo da tsarin.

Kazalika su ma mahayan ya ja hankalinsu da bin ka`idojin hanya domin kare rayukansu da na wadanda ke hanyar.