✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Laraba za a tantance Mukaddashin Alkalin Alkalai, Ariwoola

Lawan ya bukaci duk sanatoci da su halarci zaman da Majalisar za ta yi ranar Laraba.

Ranar Laraba ake sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance Mukaddashin Alkalin Alkalai na Najeriya, Olukayode Ariwoola domin tabbatar da nadinsa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ne ya sanar da haka yayin zaman Majalisar na ranar Talata.

Da wannan Lawan ya bukaci duk sanatocin da su halarci zaman da Majalisar za ta yi ranar Laraba domin tantance Mukaddashin Alkalin Alkalan.

A cewar Lawan, “Gobe Laraba, 21 ga Satumb, 2022, ita ce ranar da aka tsayar don tantancewa da kuma watakila tabbatar da nadin Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin Alkalin Alkalai na Najeriya.

An nada Ariwoola mukaddashin Alkalin Alkalan ne biyo bayan murabus da Ibrahim Tanko Muhammad ya yi daga mukamin a watan Yunin da ya gabata.

Muhammad ya yi murabus bayan da alkalan Kotun Koli suka zarge shi da tafka rashawa da kuma rashin sauke nauyin da ke kansa a matsayinsa na shugaban kotun.