✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Litinin ce 1 ga watan Sha’aban – Sarkin Musulmi

Hakan ya biyo bayan rashin ganin jinjirin sabon watan a ranar Asabar, wacce ita ce 29 ga watan Rajab.

Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Kasa (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ta bayyana Litinin, 15 ga watan Maris a matsayin daya ga watan Sha’aban na 1442.

Hakan ya biyo bayan rashin ganin jinjirin sabon watan a ranar Asabar, wacce ita ce 29 ga watan Rajab.

Sanarwar hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Masarautar, kuma Sarkin Malaman Sakkwato, Yahaya M. Boyi ya fitar da safiyar ranar Lahadi.

A ka’idar kalandar Musulunci dai, akan cika wata ya zama kwanaki 30 idan aka gaza ganin jinjirin sabon wata a daren 29 sannan washe gari ta zama daya ga sabon wata.

Watan Sha’aban dai shine wata na takwas a kalandar Musulunci kuma daga shi sai watan Ramadan wanda a cikinsa ne Musulmai a duk fadin duniya ke yin ibadar Azumi tsawon kwanakin watan.