✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar littafi ta duniya: ‘Har a nade kasa ba za a daina karanta littafi ba’

Marubucin ya ce daga nan har a nade kasa ba za a daina karanta littafi ba

An ware ranar 23 ga watan Afirilu na kowace shekara, a matsayin ranar littafi ta duniya, don tunawa da wasu manyan marubuta a duniya.

Ranar tana da matukar muhimmanci saboda a cikinta ne wasu shahararrun marubutan duniya irin su Miguel de Cervantes da Josep Pla, suka mutu.

Littafi wani Kundi ko wata ma’adana ce ta ajiye ilimi daban-daban, kama daga ilimi na addini ko boko ko siyasa ko na zamantakewa da sauransu.

Kazalika, ana amfani da littafi domin kafa hujja da wani abu da magabata suka fada a baya.

La’akari da muhimmancin irin wannan rana, Aminiya ta zanta da shahararren marubucin littattafan Hausa, Ado Ahmad Gidan Dabino, domin jin irin muhimmancin da littafai suke da shi, musamman a rayuwar Bahaushe.

Muhimmancin littafi a rayuwar Hauwasa

Ado Ahmad Gidan Dabino ya bayyana cewa, Bahaushe tun baya dama ya san darajar ilimi da littafi saboda tun kafin samuwar rubutun boko, Bahaushe yana hanyoyinsa da yake rubuce-rubucensa na littafai a rubutun Ajami.

Wanan ya sa ko da boko ya shigo bai ba shi wata wahala ba, sannan sanin darajar littafi ya sa shi ma ba a bar sa a baya ba, wajen rubuce-rubuce a harshen Hausar boko inda aka yi rubuce sosai musamman a abubuwan zamani kamar adabi tatsuniyoyi, kagaggun labarai da dai sauransu.

A cewar Ado Ahmad, a sakamakon haka Bahaushe bai dauki littafi da wasa ba, wanda kuma bai bari an bar shi a baya ba, yana da dakunan karatu da ake ajiye kundi domin adana bayanai saboda muhimmancinsu ga rayuwarsa.

Muhimmancin karatun littafi ga bunkasa al’adar Bahaushe

Daga cikin rawar da littafi ke takawa wajen bunkasa al’adar Bahaushe inji marubucin akwai ba da labaran kunne ya girmi kaka.

“Misali, kamar yaran da ba su da wayo, za a ce a koyar da su littafan tatsuniya ko wakoki ko gada, wadanda aka yi a lokacin da ba a haife su ba ko ba a haifi iyayensu ba, lokacin da aka yi wannan ababen duk suna da amfani.

“Yanzu kuma saboda rubuce-rubucen da aka yi za su dauka su karanta.

“Idan aka dauki bangaren suna ko haihuwa ko kuma rainon ciki ko daurin aure da dai sauran al’adu daban-daban, masu karatu za su samu karanta yadda al’adunsu da zamantakewarsu suke a cikin littafan da suke karatu.

“Don haka, masu karatu na samun ilimi daga abun da suke karantawa kuma ya ilmantar da su, ya sanar da su, ya wayar musu da kai a kan abin da ba su sani ba, tun kafin su zo da kuma bayan sun zo,” inji Gidan Dabino.

Yadda zamani ya shafu rubuta/wallafa littafi

A matsayin shi na marubuci kuma mawallafi sama da shekara 30, Ado Ahmad Gidan Dabino ya ce lallai yanzu rubutu na fuskantar kalubale sosai saboda rubuta littafan hausa a intanet da sauran kafafen sada zumunta na zamani.

Hakan, a cewarsa ya sa shi rubuta wata makala a kan irin wannan rubuce-rubucen littattafan a intanet, wacce za a gabatar a jami’ar Hamburg da ke kasar Jamu.

A cewarsa, akwai nakasun da rubutun Hausa ke samu a yanzu saboda yadda ake wallafa littattafai a intanet kara zube, ba tare da wata tantancewar kwararru ba.

Ya ce hakan ba karamin koma-baya ya haifar ba ga fagen rubutawa da wallafa littattafan Hausa.

Haka kuma ya ce zamani ya haifar da koma baya musamman a wajen buga littafai da ma saida su, saboda irin rubutun littafai da ake yi a kafar intanet.

Yadda marubuta ke tunkarar wannan kalubalen

Gidan Dabino ya ce kamar su da suke da tsofaffin littattafai a ajiye wadanda suka rubuta, kuma ba a riga an wallafa su a kafafen sadarwa na zamani ba, suna kokarin su shigar da aikace-aikacensu ta hanyoyin na zamani.

Ya ce idan suka shigar da su, suna kyautata zaton cewa mutane za su iya sayensu, wasu kuma za su bayar kyauta, saboda kada duniya ta dauka cewa babu tsofaffin littattafan da aka rubuta.

Makomar wallafa littafai a shekaru masu zuwa

Da ya juya kan makomar wallafa littattafai a shekaru masu zuwa, ya cebyana da yakinin ba za a taba daina rubuce-rubuce da wallafa littattafai ba har a nade duniya.

Sai dai ya ce akwai yiwuwar nan gaban a samu karancin littattafan saboda matsalar tattalin arzikin da ta addabi al’umma.

Marubucin ya ce har yanzu wasu sun fi son karatun littafi bisa wanda ake dorawa a intanet, don shi littafi ko ba komai ba zai bace ba, ba kamar intanet ba.