✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar ma’aikata: Buhari ya jefa ’yan Najeriya cikin tsaka mai wuya – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya koka kan irin halin da ma’aikatan Najeriya suka tsinci kansu a ciki. Ya yi zargin cewa ma’aikatan…

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya koka kan irin halin da ma’aikatan Najeriya suka tsinci kansu a ciki.

Ya yi zargin cewa ma’aikatan sun kara shiga tsaka mai wuya ne a zamanin mulkin Shuagaban Kasa Muhammadu Buhari.

Atiku na wadannan kalaman ne a sakonshi ga ’yan Najeriya a bikin ranar ma’aikata ta bana.

Ya koka kan abinda ya kira matsanancin halin da manufofin shugaban, musamman na bangaren tattalin arziki suka jefa kasar tare da kara tsadar rayuwa.

A cikin sakon mai taken ‘Atiku ya koka da mawuyacin halin da ma’aikata ke ciki’, wanda kakakinsa, Paul Ibe ya sanya wa hannu, Atiku ya ce, “Ma’aikatan Najeriya ba su taba shiga tasku irin wanda suke ciki yanzu ba.

“Mummunar illar da kullen Korona ya jawo musu da kuma hauhawar farashin kayayyakin da muke fuskanta shine mafi muni a tarihi. Lamarin ya yi mummunar tabarbarewar da yanzu haka sun koma rayuwar hannu baka hannu kwarya,” inji shi.

Tsohon Matimakin Shugaban Kasar ya ce matsin tattalin arzikin da gwamnatin ta jefa ’yan Najeriya a ciki ya talauta ma’aikata da dama a kasar.

Daga nan sai ya yi kira da a rage yawan kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati domin inganta rayuwar ma’aikata.