✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ranar Talata ce 1 ga watan Ramadan a Najeriya – Sarkin Musulmi

Hakan dai na nufin dukkan Musulmin Najeriya za su tashi da azumi a ranar ta Talata.

Mai alfarma Sarki Musulmi kuma shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ayyana ranar Talata a matsayin daya ga watan Ramadan na shekarar 1442 bayan hijira.

Hakan dai na nufin dukkan Musulmin Najeriya za su tashi da azumi a ranar ta Talata.

Sarkin ya sanar da hakan ne da yammacin Litinin, inda ya ce Talata, 13 ga watan Afrilun 2021 ce za ta kasance daya ga watan na Ramadan.

Ya ce hakan ya biyo bayanan da aka samu kuma Kwamitin Ganin Wata na fadarsa da sauran kungiyoyin addini suka tantance ya amince da ganin watan.

Sarkin ya yi kira ga Musulman Najeriya da su yi amfani da watan wajen yi wa kasar addu’a kan matsalolin da take fuskanta kuma a bi sharuddan kariya daga cutar Corona.

Ya kuma bukaci mawadata a cikin al’umma da su taimakawa mabukata a cikinsu musamman a wannana watan na Ramadan.

Ban da Najeriya dai, kasashen Saudiyya da Sudan da Qatar da Kuwait da Jordan da Syria da Indonesia da Malaysia da Falasdinu duk suma sun tabbatar da ganin watan.

Sai dai a kasashen Indiya da Australia da Brunei da Sri Lanka duk ba a sami ganin watan ba ranar Litinin.

Hakan dai na nufin za su cika watan Sha’aban kwanaki 30 kuma sai ranar Laraba ce za ta kasance daya ga watan Azumin a can.

A watan Ramadan dai wanda shine wata na tara a kalandar Musulunci, Musulmi a fadin duniya kan shafe tsawonsa suna gudanar da ibadar Azumi.