✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Tarin Fuka: Ganduje ya yi gargadi kan amfani da magungunan gargajiya

Za mu rika yi wa mutane gwaji da bayar da maganin cutar tarin fuka kyauta.

Gwamnatin Jihar Kano ta yi gargadi a kan amfani da magungunan gargajiya wajen magance cutar tarin fuka ko cutar tarin TB kamar yadda wasu ke kiranta.

Wannan gargadi da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi a ranar Laraba cikin birnin Kano, na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunawa da ranar yaki da cutar tarin fuka ta duniya.

Kamar yadda aka saba duk shekara, ranar 24 ga watan Maris, ita ce ranar da duniya ke tunawa da kuma sabunta yaki da cutar mai hadarin gaske.

Ganduje ya ce gwamnatinsa ta kammala shirye-shirye don gudanar da gwaji da kuma bayar da maganin cutar tarin fuka kyauta a jihar Kano.

Ya yi kira ga duk mazauna jihar da su kai kansu a duba su idan suna fama da tari har na tsawon makonni biyu ko fiye, inda ya ce gwamnatinsa ta samar da wani shiri na yi mazauna jihar gwaji da bayar da magungunan cutar kyauta.

Gwamnan, wanda ya yaba da kokarin da kungiyoyi masu bayar da tallafi ke yi wajen yaki da cutar tarin fuka da sauran cututtuka a jihar, ya ce gwamnatinsa ta ware kashi 17 cikin dari na dukkanin kasafin kudin jihar ga bangaren kiwon lafiya.

A nasa jawabin, Kwamishinan Lafiyar Jihar Aminu Tsanyawa, ya ce Kano wacce ita ce jiha mafi yawan jama’a a Najeriya, ta kuma kasance ta biyar a jerin jihohin da ke fama da cutar tarin fuka.

Tsanyawa ya ce a shekarar 2019, jihar ta samu akalla mutum 32,376 da suka kamu da cutar inda kuma aka yi sa’a an gano ta da wuri a jikin mutum 11,854 tun kafin ta yi musu wani mummunan lahani.

Kazalika, ya jaddada kudirin ma’aikatar na hada hannu da hukumomi masu bayar da tallafi don kawo karshen cutar tarin fuka a jihar.