✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar ’yacin kai Ukraine: Mun rasa kashi 20 na iyakokinmu —Zelensky

Yayin da yake kaddamar da sabuwar ranar hutun domin bikin zagayowar ranar samun ’yancin Ukraine a ranar Alhamis, Shugaba Volodymyr Zelensky nya bayyana kwarin gwiwarsa…

Yayin da yake kaddamar da sabuwar ranar hutun domin bikin zagayowar ranar samun ’yancin Ukraine a ranar Alhamis, Shugaba Volodymyr Zelensky nya bayyana kwarin gwiwarsa kan samun nasara a yakinsu da Rasha.

Shugaban ya ce duk da kasancewar safiyar ranar mai cike da tashin hankali ce sakamakon harin makami mai linzami, wannan ba zai sage guiwar kasar ba.

Shugaban dai ya bayyana hakan ne a Kiev, yayin da yake taya ’yan kasar murnar zagayowar ranar karo na farko, bayan wadda aka saba gudanarwa ranar 24 ga watan Agustan kowacce shekara.

“Kasarmu kasa ce mai cin gashin kanta, mai ’yanci, wacce ba wanda ya isa ya raba ta, kuma za ta ci gaba da kasancewa a haka har abada, ” in ji shugaban na Ukraine.

Zelensky dai ya wallafa wani bidiyo da yake wani jawabi mai ratsa zuciya game da gwagwarmayar da kasar ke yi na kwatar kanata da mamayar Rasha.

Tun da fari dai shugaban ’yan awaren Gabashin Ukraine mai goyon bayan Rasha, Denis Pushilin ya ce; lokaci ya yi da za su kwace ikon garuruwan Kharkiv, Odessa, har ma da Kiev.

Yakin kasahen biyu dai yanzu ya shiga wata na shida, kuma Zelensky ya ce kawo yanzu Ukraine ta rasa ikon kasar da kusan kashi 20 cikin dari, tare da yin kira ga kasashen yammacin turai da su samar musu da karin manyan makaman da za su dakile hare-haren Rasha da kuma kwato yankunan Ukraine da ta kwace.

Wannan sabon biki ya Zelensky ya samar da shi a 2021, a yayin da Ukraine ke kokarin yakar da’awar Rasha cewa Ukraine din kasa ce ta wucin gadi ba mai zaman kanta ba.