✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha da Ukraine sun amince su tsagaita wuta

Kasashen biyu masu makwabtaka da juna sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakaninsu.

Wakilan Kasashen Rasha da Ukraine sun amince su ci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakaninsu, bayan wata tattaunawa da suka yi sakamakon shiga tsakani da kasar Faransa da Jamus suka yi.

Babban taron, wanda manyan jami’an diflomasiyyar Faransa da Jamus suka halarta, ya hada bangarorin hudu wajen kulla yarjejeniyar zaman lafiya ta Minsk ta 2015, domin kawo karshen fada a gabashin Ukraine.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Kasar, Rasha Vladimir Putin, ya kwashe sama da sa’a biyu yana wata ganawar sirri da manyan jami’an kasar Italiya wadda take adawa da taron saboda tayar da jijiyoyin wuya kan Ukraine.

Kamfanoni sama da 16, ciki har da wani babban kamfanin makamashi ne suka halarci taron da Cibiyoyin Kasuwancin Italiya da Rasha suka shirya.

Rikici na gabashin Turai ya sa Ofishin Jakadancin Amurka da ke Ukraine ya bukaci Amurkawa mazauna Ukraine da su fara shirin ficewa, saboda fargabar mamayar Rasha.

Fargabar abin da ka iya zuwa ya dawo, ya sa Ofishin Jakadancin Najeriya a Ukraine ya gargadi  al’ummar Najeriya mazauna kasar da su guji yawo barkatari musamman a yankin Kudancin kasar wanda nan ne ya fi fama da tashin-tashina.

Barazanar yaki tsakanin Rasha da Ukraine na kara kamari, inda Rasha ta jibge sojoji da tankokin yaki da manyan makamai a kan iyakokinta da Ukraine.

Sai dai sauran manyan kasashen duniya sun yi ta fadi tashin ganin an sulhunta kasashen biyu da suka jima suna tayar da jijiyon wuya.