✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha ta hamrata amfani da Facebook da Instagram

Kotun ta ce kafafen sadarwar na yada labarun karya kan mamayar Ukraine da Rasha ta yi.

Wata kotu a birnin Moscow ta haramta amfani da Facebook da Instagram a Rasha, bayan da ta ayyana ayyukansu a matsayin masu tsauri.

Kamfanin dillacin labarai na Tass na kasar Rasha, ya ce alkalin kotun, Olga Solopova, ya yanke hukuncin ne bayan shigar da kara da aka yi kan kamfanin Meta, mamallakin Facebook da Instagram.

Ofishin Babban Mai Gabatar da Kara na Rasha, ya ce ana yada abubuwan karya game da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ta kafofin sadarwar.

Tun da farko an toshe Facebook da Instagram a Rasha kan abin da Fadar Kremlin ta kira yada labaran kanzon kurege.

Alkalin kotun ya ce hukuncin bai shafi kafar WhatsApp ba, mallakin kamfanin Meta.

Tun bayab mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine take ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashe da dama na Yammacin Turai, amma hakan bai sanya shugaba Putin ya saduda ba.