✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rasha ta harba makami mai linzami a filin jirgin saman Ukraine

Rasha ta harba makamin mai linzami wanda ya lalata titin tashin jirgin saman yankin.

Rasha ta harba wani makami mai linzami a filin jirgin saman birnin Odessa da ke Kudancin kasar Ukraine, wanda hakan ya yi sanadin lalacewar titin saukar jirage.

Sai dai babu wanda ya jikkata, kamar yadda gwamnan yankin Maxim Marchenko ya bayyana a shafinsa na Telegram.

Rasha ta yi luguden wuta a kan birnin Kharkiv, birni na biyu mafi girma a Ukraine a ranar Asabar.

Su ma dakarun Ukraine din sun samu galaba a wasu yankunan birnin, a daidai lokacin da Amurka ke zargin Shugaban Rasha, Vladimir Putin da zalunci.

Ko da yake dakarun Ukraine sun sake karbe iko da Kharkiv, Rasha ta barnata birnin da hare-haren da take kai wa ta sama ba kakkautawa.

Wannan na zuwa ne bayan da Rasha ta tabbatar da cewa ita ta kai hari ta sama a kan birnin Kyiv, a daidai lokacin da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ke ziyara a ranar Alhamis.

Tashar Rediyon da Amurka ke daukar nauyi ta Free Europe/Radio Liberty ta ce ma’aikaciyarta, Vera Gyrych ta mutu a lokacin da makami mai linzami na Rasha ya fada gidanta.

Kasashen biyu na ci gaba da gwabza yaki a tsakaninsu, tun bayana da Rasha ta kaddamar da yaki a kan Ukraine a watan Fabrairun 2022.