✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha ta kashe mana sojoji kusan 13,000 – Ukraine

Amma sun ce wadanda Rasha ta rasa sun ninka nata sau bakwai

Wani jami’in gwamnatin Ukraine ya ce akalla sojojin kasar 13,000 ne Rasha ta kashe musu tun bayan fara yakinsu kimanin wata tara da suka wuce.

Kalaman na Mykhailo Podolyak, wani Hadimi ga Shugaban Kasar, Volodymyr Zelenskyy, su ne alkaluma na baya-bayan nan da aka fitar kan yawan dakarun da aka kashe, tun bayan 9,000 da Shugaban Sojojin Kasar ya bayyana a watan Agustan da ya gabata.

“Muna da alkaluma a hukumance daga manyan Shugabannin Sojoji, kuma yawan wadanda aka kashe ya kai tsakanin 10,000 zuwa 12,500 ko ma 13,000,” kamar yadda Mykhailo ya shaida wa gidan talabijin na Ukraine ranar Alhamis.

Ya kuma ce adadin wadanda suka jikkata a yakin kuma ya haura na wadanda aka kashe din.

Sai dai har zuwa yanzu, Rundunar Sojin Ukraine ba ta tabbatar da alkaluman ba. Amma Hadimin ya ce Shugaba Zelenskyy zai sanar da cikakken adadin da kansa, idan lokacin da ya dace a yi hakan ya yi.

A watan Satumban da ya gabata dai sojojin na Ukraine suka matsa kaimi wajen mayar da martani kan hare-haren Rasha, lamarin da ya ba su nasara har suka kwato birnin Kherason da Rashar ta kwace.

A baya dai, Shugaban Amurka, Joe Biden da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, wanda yanzu haka yake birnin Washington DC, sun yi alkawarin ci gaba da tallafa wa Ukraine, tare da yin Allah-wadai da mamayar Rasha a kanta.

To sai dai yayin da ake wata tattaunawa da shi ranar Laraba, shugaba Zelenskyy ya yi ikirarin cewa yawan mutanen da Rasha ta yi asara sun ninka na Ukraine har kusan sau bakwai.