✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha ta sanya wa Boris Johnson takunkumin shiga kasarta

Rasha ta ce za ta sake sanya wa wasu shugabannin takunkumin shiga kasarta

Rasha ta haramta wa Firaministan Birtaniya, Boris Johnson, shiga kasarta saboda mara wa Ukraine baya da kasar shi ta yi a yakin da take yi tsakaninta da Ukraine.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha, ta ce matakin ya shafi Sakataren Harkokin Waje, Liz Truss, da na tsaro Ben Wallace da wasu mambobin gwamnati da ‘yan siyasar Birtaniya.

Rasha ta dauki matakin ne saboda matakin nuna kiyayya da gwamnatin Birtaniyya ta dauka, musamman na sanya takunkumi kan manyan jami’anta, kamar yadda sanarwar da ma’aikatar ta fitar.

Kazalika ta kuma ce nan ba da jimawa ba za ta kara yawan sunayen wadanda za ta sanya cikin jerin wadanda za ta haramta wa shiga kasar.

Tuni dai Rasha ta haramta wa Shugaban Amurka Joe Biden da wasu manyan jami’an Amurka shiga kasarta.

Rashan ta dauki matakin ne don tauna tsakuwa kan yadda kasashen yammacin turai ke ci gaba da sanya mata takunkumin kan mamayar da ta yi wa Ukraine.

Tun bayan fara yakin a watan Fabrairun shekarar nan, dubban mutane daga Rasha da Ukraine sun rasa rayukansu, yayin da kuma miliyoyin mutane suka tsere daga Ukraine don tsira da rayukansu.