✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha ta soma take-taken janyo Belarus cikin yaki —Ukraine

An harba wasu makami masu linzami daga Belarus zuwa iyakar Arewacin Ukraine.

Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Ukraine ta ce Rasha na kokarin janyo Belarus cikin yakin da ke wakana a tsakaninsu, bayan da aka harba wasu makami masu linzami daga Belarus din zuwa iyakar Arewacin Ukraine.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Faceboook, Hukumar ta ce an harba makamai masu linzami har guda 20 a ranar Asabar a kan kauyen Desna da ke yankin Chernigiv na Arewacin kasar.

Ta kara da cewa makamai masu linzamin sun fada a wurare da ke Arewacin birnin Kyiv da yankin Sumy, tana mai cewa ta gano cewa Rasha na kokarin janyo Belarus cikin rikicin ne.

Luguden wutar na da karfi, sai dai babu wanda ya jikkata a sakamakonsu, a cewar hukumar tattara bayanan sirrin.

Dakarun Ukraine sun janye daga Donbas

A bayan nan ne mahukuntan Ukraine suka umarci dakarun sojin kasar su janye daga sassan Severodonetsk da ke yankin Donbas, bayan shafe makwanni suna gwabza yaki da Sojin Rasha da ke kokarin kwace iko da babban birnin na gabashin kasar.

Janyewar dakarun na Ukraine daga Severedonetsk na zuwa ne bayan karfafa hare-haren Sojin Rasha a yankin na Donbas a ci gaba da kokarin kwace iko da yankin mafi girma a Gabashin Ukraine dai dai lokacin da kungiyar EU ta bai wa kasar damar zama mambarta.

Tun bayan faro mamayar ta Rasha ga Ukraine a karshen watan Fabarairu, kasar ta tsohuwar tarayyar Soviet ta mika bukatar shiga EU don zame mata kariya daga barazanar Rasha, sai dai duk da matakin amincewar kungiyar hakan bai hana makwabciyartata ci gaba da mamaye manya kuma muhimman yankunan Kiev ba.

Bayan fatattakar sojinta a Kiev, Rasha ta karkata ilahirin karfinta zuwa yankin na Donbas da ke Gabashin Ukraine inda ta ci gaba da kwace kananun garuruwa da birane gabanin kai wa ga Severedonetsk da dakarun na Moscow ke gab da kwacewa.

Gwamnan Lugansk, yankin da ya kunshi har Severedonekts Sergiy Gaiday ya ce duk da asarar rayukan da ake musu dakarun Rasha na ci gaba da kutsawa sassan yankin wanda ke nuna dole su janye dakarunsu.

A cewar gwamnan dakarun Rasha sun lalata kashi 90 na yankin kuma zuwa yanzu yankunan masana’antu ne kadai ke karkashin ikon Ukraine.