✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha ta yi gwajin wani ‘hatsabibin’ makami mai linzami

Putin ya ce makamin zai sanya abokan gabar Rasha shiga hankalinsu.

Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya ce kasarsa ta yi nasarar gwajin wani makami mai linzami mai suna Sarmat da ke cin dogon zango daga nahiya zuwa nahiya.

Yayin wani jawabi ta gidan talabijin din kasar, Putin ya ce yana taya sojoji murna kan nasarar gwajin makami mai linzami na Sarmat da suka yi a ranar Laraba.

A wata sanarwa, Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce an yi gwajin cikin nasara a garin Plesetsk a arewacin kasar.

Putin ya ce sabon makamin da ke goya nukiliya na iya cin dogon zango tare sa yin barna mai muni idan aka yi amfani da shi.

Ya kara da cewa wannan makami na musamman zai karfafa sojojin kasar da tabbatar da tsaron Rasha daga barazanar kasashen waje tare da sanya wando da abokan gabar Rasha.

Makamin na Sarmat, wanda masu sharhi a Yammacin Turai suka yi wa lakabi da ‘Satan 2’ na daga cikin sabbin makamai masu linzami da Shugaba Putin ya bayyana a matsayin ‘hatsabibai’ kuma sun kunshi makaman Kinzhal da Avangard masu matsanancin gudu da ya ninka na sauti sau biyar.

A watan da ya gabata, Rasha ta ce ta yi amfani da makami mai linzami samfurin Kinzhal wajen kai hari a Ukraine, wadda ta mamaya tun a ranar 24 ga watan Fabrairu.