✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha za ta bai wa Afghanistan man fetur da alkama na shekara 1

Rasha ta kulla wata yarjejeniyar bai wa gwamnatin Taliban a Afghanista man fetur da dizel da kuma alkama na tsawon shekara guda. A karkashin yarjejeniyar,…

Rasha ta kulla wata yarjejeniyar bai wa gwamnatin Taliban a Afghanista man fetur da dizel da kuma alkama na tsawon shekara guda.

A karkashin yarjejeniyar, Rasha za ta ba gwamnatin Taliban kimanin tan miliyan daya na man fetur da man dizel da kuma ton miliyan daya na alkama a duk shekara.

An sa hannu kan yarjejeniyar ne bayan da wani kwamitin kwararru na ’yan Afgahanistan su ka yi makwanni suna tattaunawa da jami’an gwamnatin Rasha a Moscow.

’Yan kwamitin sun kuma zauna a can har sai da Minista Azizi ya kai ziyara a watan Yuli.

Mukaddashin Ministan Ciniki da Masana’antu na gwamnatin Taliban, Haji Nooruddin Azizi ne bayyana haka a hirarsa da Reuters ranar Talata.

Yarjejeniyar ta wucin gadi ce, a matsayin gwaji, ana kuma sa ran ta yi aiki kafin bangrorin biyu su sake sa hannu kan wata yarjejeniyar ta tsawon lokaci a nan gaba.

Wannan yarjejeniya ita ce ta farko ta fuskar tattalin arziki da Afghanistan ta kulla da wata kasa tun lokacin da Taliban ta kwace mulki a kasar a shekarar 2021.

Rasha ba ta amince da Gwamantin Taliban ba a hukumance, amma ta karbi bakuncin shugabanin  Taliban a kasarta na wani lokaci kafin su kwace gwamnati.

Sannan kuma, Ofishin Jakadancin Rasha na daga cikin ’yan kadan da ba su rufe ba a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.