✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha za ta maka FIFA da UEFA a kotun da’ar wasanni

Rasha ta kalubanci dakatarwar da FIFA da UEFA suka yi wa kungiyoyin wasanta

Hukumar Kwallon Kafa ta kasar Rasha ta ce za ta garzaya kotun da’ar wasanni (CAS) don kai kukanta game da dakatar da ita da kungiyoyinta shiga harkokin kwallon kafa a duniya.

A farkon makon nan ne hukumomin kwallon kafa na FIFA da UEFA suka sanar da dakatar da Rasha da kungiyoyin kwallon kafar kasarta shiga kowace irin gasa har sai yadda hali ya yi, saboda mamaye kasar Ukraine.

Sai dai hukumar kwallon kafar Rasha ta yi martani da cewa za ta shigar da kara a kotun da’ar wasannin don kalubalantar matakin.

A yanzu Rasha na son a ba wa tawagarta damar buga wasan neman gurbin zuwa gasar cin Kofin Duniya, a kuma kyale tawagar matan kasar zuwa gasar cin Kofin Nahiyar Turai ta Euro 2022 da za a yi a Ingila.

Tuni UEFA ta sallami kungiyar kwallon kafa ta Spartak Moscow daga gasar EUROPA, wanda hakan ya bai wa abokiyar karawarta RB Leipzig damar tsallakewa zuwa zagayen kwata-fainal.

FIFA da UEFA sun dauki matakin ne bayan Rasha, da goyon bayan Belarus, ta kutsa tare da kai hare-hare a kasar Ukraine makon da ya wuce.

Rasha na ci gaba da fuskantar takunkumi da kyama daga sauran kasashen duniya kan yadda ta far wa kasar Ukraine da yaki, lamarin da ya yi sanadin salwantar rayukan mutane da dama.