✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rashawa: Bankin Duniya ya kakaba wa kamfanoni 4 a Najeriya takunkumi

Aikata laifin cin hanci a ayyukanmu ba karamin lalata martabar mu zai yi a idon Duniya ba.

Bankin Duniya ya kakakaba wa wasu kamfanoni 4 da wasu daidaikun mutane uku a Najeriya takunkumi, bisa samunsu da aikata laifukan cin hanci da rashawa.

Wannan dai ya bulla ne cikin rahoton takunkumin karshen shekara da Bankin ya saba fitarwa, da ya fara daga 1 ga watan Yulin shekarar 2021 zuwa Yunin 2022.

Kamfanoni hudu daga ciki dai Bankin Washington na Amurka ne zai bincike su, sai kuma wasu biyu da Bankin Raya Afirka ya sanya wa takunkumi da amincewar wasu kungiyoyi masu zaman kansu, ciki har da Bankin Duniyar.

Wani dan Najeriya mai suna Salihu Tijjani  na daga cikin daidaikun da Bankin ya sanya wa takunkumin tsawon shekaru biyu da wata biyu, sai Isah Kantigi da aka sanyawa takunkumin shekaru biyar.

Sauran sun hada da Aminu Moussali tsawon shekaru biyu da watannin 10, amma zai ci gaba da gudanar da ayyukansu idan ya amince da sharudan Bankin na tsawon shekara daya da watanni shida.

Duk wanda ya samu makamncin wannan takunkumin, zai ci gaba da gudanar da aikinsa matukar ya amince da sharudan da Bankin ya gindaya masa.

Da yake jawabi kan rahoton, Shugaban Bankin David Malpass, ya ce aikata laifin cin hancin a ayyukansu ba karamin lalata martabar su zai yi a idon Duniya ba, musammn yadda suke kasafta kudaden gudanar da ayyukansu.

“Saboda haka, yana da muhimmanci a san tsarin sanya takunkumimn Bankin, kasancewar yana taka muhimmiyar rawa ga kokarin da cibiyoyinmu ke yi na kula da tsaftar kudaden da muke bayarwa,” in ji shi.