✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rashawa: Kotu ta yanke wa Farouk Lawan daurin shekara 7

Kotu ta daure tsohon dan majalisar bisa laifin cin hanci da aka same shi da shi.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke hukuncin daurin shekaru bakwai kan Honarabul Farouk Lawan, tsohon Shugaban Kwamitin Tallafin mai a Majalisar Wakilai.

Kotun ta daure Lawan bayan samun shi da laifin karbar cin hanci daga attajirin dan kasuwar nan, Femi Otedola, a lokacin da yake shugabantar kwamitin binciken badakalar tallafin kudaden mai a shekarar 2012.

  1. ‘Malamai 3,264 ne ke karbar albashin gwamnati suna aiki a makarantun kudi a Kano’
  2. Shugaban Karamar Hukuma ya mutu a Legas bayan ya sake lashe zabe

Mai Shari’a Angella Otaluka ce ta yanke wa Lawan hukunci a ranar Talata bayan tabbatar da wasu laifuka uku da ake zarginsa da su.

An yanke masa hukuncin shekara bakwai inda ya yanki tikitin cin sarka ta shekara biyu kan laifi na daya dana biyu sai kuma daurin shekara biyar kan laifi na ukun.

Kazalika, Kotun ta bukaci Lawan da ya mayar wa da Gwamnatin Tarayya dala 500,000 da ya karba daga hannun Otedola.

Lawan wanda ya shugabanci kwamitin na wucin gadi ya nemi cin hancin zamanin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.

Otedola ya zargi Lawan da neman dala miliyan 3 daga wani kamfaninsa mai suna Zenon Petroleum & Gas Limited domin a cire shi daga kamfanonin da ake bincike.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuffuka (ICPC), ta tuhume shi da karbar cin hancin Dala 500,000 daga Otedola amma dan majalisar ya musanta zargin da ake masa.