✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashawa: Mun kwato sama da N500m a Kano — Muhyi

Mun kuma kwato filaye sama da 400 a Jihar Kano.

Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Rashawa a Jihar Kano (PCACC), ta sanar da kwato sama da naira miliyan dari biyar a fadin jihar.

Shugaban Hukumar, Muhuyi Magaji Rimingado ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin hukumar ranar Laraba.

Yayin taron na bayyana nasarorin da Hukumar ta samu a shekarar 2020 da ta gabata da kuma rubu’in farko na bana, Muhuyi ya ce sun kuma kwato filaye sama da 400 wanda tuni an mayar wa da mamallakansu na ainihi.

“Mun samu korafi sama da 2,000 wanda kaso 70 daga cikinsu an yi maganin matsalolin.

“Mun kwato filaye sama da 400, tare da kwato kayan tallafin COVID-19 da aka boye, sannan mun hana boye man fetur da kuma karin farashin kayan abinci,” in ji Rimin Gado.

“Duk da tarin nasororin da muka samu, amma muna fuskantar kalubale na katsalandan da wasu masu madafan iko ke yi wa ayyukanmu.

“Sannan kuma muna fuskantar kalubale wajen kudaden da za a gudanar da wasu ayyuka a Kananan Hukumomi 44 da muke da su a fadin Kano,” a cewarsa.

Rimin Gado, ya bayyana aniyar hukumar na yin aiki kafada da kafada Hukumar da EFCC da ta ICPC, don ciyar da jihar Kano gaba wajen yaki da cin hanci.