✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Rashin adalcin shugabanni ne tushen matsalar rashin tsaro a Najeriya’

Wani malamin addinin Kirista ya bayyana rashin adalcin shugabanni da cewa shi ne ummul-aba’isun da ke kawo tabarbarewar tsaro da aikata ta’addanci a Najeriya. Rabaran…

Wani malamin addinin Kirista ya bayyana rashin adalcin shugabanni da cewa shi ne ummul-aba’isun da ke kawo tabarbarewar tsaro da aikata ta’addanci a Najeriya.

Rabaran Isaac Gbadero na na Majami’ar First Baptist da ke Sabon Garin Zariya ne ya bayyana haka a sakonsa na bikin Kirsimeti na bana ga mabiyansa.

A cewarsa, dukkan bala’o’in da Najeriya ke fama da su a halin yanzu rashin adalcin shugabanni ne da muka sami kanmu a ciki.

Ya gargadi al’umma da su koma ga Allah tare da neman afuwarSa bisa laifuffukan da suke aikatawa.

A ranar Asabar ne dai Kiristocin Najeriya suka bi sahun dimbin takwarorinsu a fadin duniya domin bikin ranar Kirsimetin na bana.

Ana dai bikin ne don tunawa da ranar da aka haifi Annabi Isa (A.S), wato Yesu Almasihu.