✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Rashin hukunta sojojin da suka kashe Sheikh Aisami na damun mu’

Su yi wa Allah su rika sanar da mu a duk lokacin da za a yi zaman kotu.

Iyalan fitaccen malamin Islama da wasu sojoji suka kashe bayan sun yi masa fashi, Sheikh Goni Aisami, sun bayyana damuwa ganin cewa har yanzu ba a yanke wa sojojin hukunci ba.

A kokarinsu na neman hakkin mahaifinsu da aka yi wa kisan gilla a kwanakin baya, iyalan sun bayyana damuwarsu ga yadda suka ce har yanzu ba a gurfanar da wadanda ake zargi da kashe mahaifin su ba kusan kwanaki Hamsin da aikata hakan.

Wannan korafi dai ya fito ne daga daya daga cikin iyalan malamin, Abdullahi Goni Aisami, a ganawarsu da Aminiya dangane da jan kafar da hukumomin tsaro da na shari’a ke yi bisa wannan shari’a da ake yi ga sojan da ya halaka musu mahaifi haka siddan.

A kwanakin baya ne dai wani soja da malamin ya rage wa hanya daga garin Nguru ake zargi da harbe shi domin ya sace motarsa yayin da malamin ke kan hanya daga Kano zuwa garin su na Gashua.

Malam Abdullahi Aisami ya ce, su iyalan malam lura da cewar, suna alhinin kisan gillar da aka yi wa mahaifisu amma kuma duk da haka sai suka ga ana tafiyar hawainiya wajen gudanar da shari’a kan wadanda suka kashe shi, wadda abin yana daure musu kai.

Dan malamin, Abdullah Aisami

Abdullahi Goni Aisami ya ce sun shiga cikin tashin hankali matuka  saboda rashin jin wata kwakkwarar hujja daga hukumomi kan abin da ya sa aka ki hukunta mutanen da suka aikata wannan aika-aika kan mahaifi su.

“Muna cikin matsanancin bakin ciki da takaici, su daga bangaren matan malam, hankalinsu ya fi na kowa tashi saboda suna ganin kamar an ma ki yin hukuncin ne haka kawai ko saboda wata manufa.”

A cewarsa, labarin da ya ji a BBC kuwa cewar, wai har an kai wadanda suka aikata wannan a aika-aika kan mahaifi su kotu.

“A gaskiya mu ba mu ma da labarin har an kai su kotu wadda kuwa in da har babu wata manufa ya kamata a ce an shaida mana batun zuwa kotu don muma mu rika sanar da ‘yan uwa da magoya bayan malamin kan hakan don su rika kwantar da hankalin su.

“Don haka mu iyalan Malam Goni Aisami muna rokon hukumomin da abin ya shafa dangane da wannan lamari na hukunta makasan mahaifin mu.

“Su yi wa Allah a duk yayin da za a shiga kotu tare da wadannan mutane da suka kashe mahaifin mu a sanar da mu don mu bibiyi lamarin hakan zai iya samar mana nutsuwa.”

Ta bangaren hukumar tsaro kuwa, kakakin rundunar ‘ƴan sanda na jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkareem ya ce bayan sun gama bincike suka tura wa hukumar shari’a ta jihar domin tabbatar da cewa an gurfanar da wadannan sojoji guda biyu gaban kuliya.

“An yi nasarar haka, inda ranar 19 ga watan Satumba aka gabatar da su a gaban kotu, kuma kwamishina da kansa ya zama lauya mai gabatar da kara na gwamnati,” in ji Dungus.

“Ya gabatar da hujjojinsa da shaidunsa gaba daya a gaban kotu inda wadanda ake zargi suka ce su ba su da laifi, sannan aka tsaya daga nan aka rufe karar, za a sake sauraron shari’ar a zama na biyu in rai ya kai.”

DSP Dungus ya kara da cewa, lokacin da aka yi zaman shari’ar kotunan Najeriya suna hutu, kuma “muna tunanin idan sun dawo hutu, za su sanar da mu ranar da za a sake dawo da sojojin zuwa kotun don ci gaba da hukuncin da ya dace da masu laifin irin ya nasu.