✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin kara aure ke jawo karuwanci

Fitaccen dan kasuwa, wanda ya yi fice wajen kara aure, wanda yafito daga yankin Kudu maso Kudu, Ned Nwoko ne ya bayyana haka yayin zantawa…

An bayyana cewa zama da mace daya da mazan Kudancin kasar nan ke yi na ci gaba da haifar wa ’yan matan yankin yin gararamba, suna bin maza domin su samu abin da za su sanya wa bakinsu.

Fitaccen dan kasuwa, wanda ya yi fice wajen kara aure, wanda yafito daga yankin Kudu maso Kudu, Ned Nwoko ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema lanarai.

Nwoko ya ci gaba da cewa, “idan maza a Kudancin kasar nan za su rika auren mata hudu da yaranmu ba za su rika yin yawon karuwanci ba suna neman abin da za su sanya wa bakinsu.”

Ned Nwoko, wanda tsohon dan majalisa ne ya yi mamakin irin yadda ’yan Kudu suka rike akidar auren mace daya su zauna da ita.

“Kara aure ba wata matsala ba ce. Hakan zai kawo karuwar iyali da rage yawon fasikanci da ’yan matan Kudu ke yi.”

Ya kuma bayyana matukar damuwa da irin yadda ’yan mata a Kudu suke rayuwarsu, inda ya ce “abin na ba ni tsoro da takaici.”

A kan haka ya doka misali da ’yan Arewa, inda ya ce, “a Arewa mafi karanci, mutum a ce matarsa daya. Daga mai biyu sai uku da hudu. Abin da ba mu da shi a Kudu ke nan.”