✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rashin kishi ne kiran gwamnati ta bude iyakoki – Masani

Rashin kishi ne kiran gwamnati ta bude iyakoki – Masani

Daraktan Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Muhammad Faguji Ishiyaku ya ce, rashin kishin kasa ne kiraye-kirayen da wasu ke yi ga gwamnati cewa ta bude iyakokin kasa saboda a shigo da abinci daga kasashen waje don magance hasashen yiwuwar aukuwar yunwa a shekarar 2023.

Farfesa Muhammad Faguji Ishiyaku ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilinmu a Zariya, inda ya ce bude iyakokin kasa ba abin da zai haifar sai matsala da ta wuce wadda manoma suke fama da ita ta rashin tabbas a shekarar 2023.

Farfesa Faguji Ishiyaku ya ce, a maimakon kiran a bude iyaka kamata ya yi gwamnati ta umarci Hukumar Inshorar Amfanin Gona ta kasa ta tallafa wa manoman da ambaliyar ruwa ta shafa domin su samu karfin gwiwar ci gaba da aikin noma don ciyar da kasa gaba ta fannin noma.

Kwararren masanin aikin gonar ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi su gina kananan madatsun ruwa a yankunan karkara domin kare manoma daga fadawa cikin matsalolin fari da kuma ambaliyar ruwa da take aukuwa shekara da shekaru, kamar yadda ta auku a bana, inda ya ce samar da madatsun ruwan zai magance irin hasashen da ake yi na yiyuwar yunwa a 2023.

Daraktan ya ce, sun samar da ingantattun irin masara da wake masu jure fari da ruwa ta yadda manoma za su rage asarar da suke yi kuma a bana cibiyar za ta fitar da sabon irin dawa ga manoma.

Ya shawarci manoma su rika amfani da ingantattun iri domin samun yabanya mai kyau ta yadda za su samar da abinci ga kasa har su fitar zuwa kasashen waje.

Game da ambaliya Farfesa Faguji Ishiyaku ya shawarci manoma su rika aiki da shawarar kwararrun irin Hukumar Kula da Yanayi ta kasa da masana aikin gona domin kauce wa shiga matsalolin a yayin aikin noma a 2023.