✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rashin lafiya ne ya kashe Mahsa Amini, ba ’yan Hisbah ba —Iran

Gwamnatin Iran ta ce binciken da aka gudanar kan rasuwar Mahsa Amini a hannun jami'an Hisbah a kasar ya nuna a rashin lafiya ne ya…

Gwamnatin Iran ta ce binciken da aka gudanar kan rasuwar Mahsa Amini,  a hannun ’yan Hisbah a kasar ya nuna a rashin lafiya ne ya yi sanadin mutuwar ba duka ba.

A makonni uku da suka gabata ne aka yi ta bore a kasar da sauran wurare bisa zargin ’yan Hisbah sun lakada mata duka har ta mutu a hannunsu, saboda ta yi shigar da ta saba Musulunci.

Hukumar kula da harkokin shari’a ta Iran ta fada a ranar Juma’a cewa “Mutuwar Mahsa Amini ba ta alaka da bugun kai ko wata gaba a jikinta.”

Hukumar ta ce, mutuwar Mahsa Amini, wacce sunanta da harshen Kurdawa Jhina, na da alaka da “tiyatar kwakwalwa da aka yi mata tun taba da shekaru takwas.”

Iyayen marigayiyar sun shigar da kara a kan jami’an da lamarin ya shafa, kuma daya daga cikin ’yan uwanta da ke zaune a Iraki ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa ta rasu ne sakamakon wani mummunan bugun da aka yi mata.

Wasu ’yan mata kuma sun rasa rayukansu a zanga-zangar, amma Amnesty International ta ce Iran na tilasta wa iyalansu furuci a gidajen talabijin domin su wanke kansu daga alhakin mutuwarsu.

A ranar 16 ga watan Satumba ce Mahsa ta rasu, kwana uku bayan ’yan Hisbah kasar sun damke ta a Tehran, babban birnin kasar, kan laifin yin shigar da ta saba Musulunci.

Labarin rasuwar tatar ya haifar da tarzoma a kasar, wadda ta yi sanadin mutuwar mutum baya ga wasu da dama da jami’an tsaro suka tsare.

Duk da karfin soji da jami’an tsaro suka yi amfani da shi wajen murkushe tarzomar, zanga-zangar da mata suka jagoranta ta ci gaba har na tsawon kwana 21.