✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin na’urar kashe gobara ya jawo konewar kamfanin kayan daki a Kano

Gobara ta yi barna a wani kamfanin kera kayan daki da ke titin Murtala Muhamamd a Kano, sakamakon rashin aikin na’urar kashe wuta

Gobara ta yi barna a wani kamfanin kera kayan daki da ke titin Murtala Muhamamd a Kano, sakamakon rashin aikin na’urar kashe wuta.

Wani makwabcin kamfanin da lamarin ya faru a idonsa mai suna Udo Jonah ya ce ranar Laraba ne lamarin ya faru, wanda ya sa ma’aikatan ciki ihun neman agaji.

“Da misalin karfe 10:00 na safe ne gobarar ta fara, ina fitowa na ga mutane na ihun neman agaji, ashe na’urar kashe gobarar da kamfanin ke da ita ce ba ta aiki, ballle ta kashe wutar tun ba ta yi karfi ba.

“Sannan su ma masu kashe gobarar ba su zo a kan lokaci ba, don haka kasa da sa’a daya gobarar ta illata kamfanin.

“Mun dai taimaka an ciro dan abinda aka samu daga kamfanin”, in ji Jonah.’

A nasa bangaren Kakain Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi Yusuf ya ce “Mun samu kiran ne da misalin karfe 10:58.

“Mutanennmu sun kuma zo sun kashe, kuma an samu nasarar fitar da wasu kayayyakin.

“Muna zargin wata na’aura mai amfani da wutar lantarki ce ta haddasa gobarar amma dai muna kan bincike.

“Ba za mu iya tantance ainihin asarar da aka yi ba, domin masu kamfanin ne za su iya sani.”

Aminiya ta tattaro cewa ya zuwa yanzu ba a samu asarar rai ko jikkata ba, sannan ana kwashe wasu kayayyakin da suka yi saura da taimakon mutanen da ke wajen.

 

Daga Rahima Shehu Dokaji; Salim Umar Ibrahim da Aminu Naganye (Kano)