Daily Trust Aminiya - Rashin Tsaro: ‘A ci gaba da girke dakaru a Jihar Sakkwato’
Subscribe

Dakarun Soji

Rashin Tsaro: ‘A ci gaba da girke dakaru a Jihar Sakkwato’

Shugabannin Kungiyar Matasa da ta Dalibai, Aliyu Gadanga da Aminu Muhammad, sun yi kira da aka ci gaba da tsananta ayyukan dakarun soji a wuraren da ke fama da hare-haren ’yan bindiga a jihar Sakkwato.

Sun yi kiran ne a lokuta daban-daban yayin ganawa da manema labarai na Jaridar Daily Trust yayin bikin Ranar Zaman Lafiya ta Duniya.

Kiran neman a ci gaba da girke dakaru ba zai rasa nasaba ba da kisan gillar da aka yi wa wasu manyan jami’an ’yan sanda biyu da kuma garkuwa da aka yi da wasu matan aure uku a baya-bayan nan a Gidan Madi da ke Karamar Hukumar Tangaza ta Jihar.

Shugabannin kungiyoyin biyu sun yaba wa Rundunar Sojin Najeriya da kuma Gwamnatin Jihar dangane da fadi-tashin da suke yi na tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a Gabashin Jihar.

A cewarsu, irin wannan aiki na hadin gwiwa shi ake bukata domin tsarkake Arewacin Jihar daga hare-haren ’yan daban daji.

Sun kuma shawarci matasa da daliban jihar da su mara wa sojoji da gwamnati baya a yakin domin tabbatar da aminci a zukatan al’umma.

“Dole ne mu sa ido kuma tallafa wa gwamnati da sojoji a kokarin da suke yi na kawo zaman lafiya mai dorewa a jihar,” inji Kwamaret Muhammad.

Ya kuma shawarci matasa da su tona asirin duk wani mai laifi sannan su rika kai rahoton duk wani motsi na rashin yarda da suka gani zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa.

More Stories