✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin tsaro: Buhari na bukatar taimakon kasashen waje —Ortom

Ortom ya ce daidai ne Najeriya ta nemi taimakon kasashen waje kan matsalar tsaro.

Gwamnan Binuwai, Samuel Ortom, ya ce kashe-kashen da ake yi a kulla-yaumin a Najeriya ya nuna cewa abun ya yi wa Gwamnatin Tarayya yawan da ba za ta iya magance matsalar tsaron da kasar take fusktanta ba.

Ortom ya ce ba laifi ba ne Gwamantin Tarayya ta nemi taimakon kasashen waje wajen magance matsalar tabarbarewar tsaron da ke kara ta’azzara.

A cewarsa, ayyukan Boko Haram da sauran ’yan ta’adda na ci gaba a Najeriya ne saboda ba ta yi wa tufkar hanci ba ta hanyar samar da ingantanccen ilimi ga ’yan kasar.

“Da suna da ilimi, da shagaltuwa za su yi da abubuwan da za su amfane su, ba su rika aikata fasadi ba a cikin kasa,” inji shi.

Don haka ya ya bukaci Shugaba Buhari da gaggauta neman taimakon kasashe domin ganin a shawo kan matsalar.

A cewarsa, mummunan yanayin da Najeriya ta tsinci kanta abin kunya ne, a yayin da gwamnonin jihohin da ke fama da matsalar ke cin tashin hankali.

Ya ce duk da haka, Allah bai yi watsi da Najeriya ba, don haka ya bukaci shugabanni da su hada kai wajen samar da adalci da daidaito a kasar.

Ya yi bayanin ne a wurin bude Makarantar Sakandaren ’Ya’yan Sojoji da ke Effurun, a Jihar Delta.

“Na fadi haka ne saboda yakinin da nake da shi a kan ilimi, domin idan za ka inganta al’umma dole sai ka ba su ingantaccen ilimi, shi ya sa nake jinjina wa Gwamna Okowa saboda gina wannan makaranta mai inganci,” inji shi.