✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rashin tsaro: Mutanen Tsafe sun tare hanyar Gusau zuwa Funtua

Masu zanga-zangar sun ce ba za su bar wurin ba sai an biya musu bukata.

Mazauna kauyukan da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara sun tare babbar hanyar Gusau zuwa Funtua domin nuna bacin ransu kan yadda hare-haren ’yan bindiga ke ci gaba da jefa rayuwarsu a cikin kunci.

Masu zanga-zangar da suka hana ababen hawa wucewa, sun koka da cewa duk ta katse layukan sadarwa a jihar, ’yan bindiga sun hana su zuwa gonakinsu, don haka ba za su bar kan babbar hanyar ba har sai an biya musu bukatunsu.

Wani daga cikinsu, wanda ya ce sunansa Aliyu ya ce, “Har yanzu ’yan bindiga ne suka mamaye kauyukan Yankuzo, Yan ware, Tafkin Kazai, Hayin Alhaji Yartalata da ke Gabashin Tsafe.

“Duk da cewa an samu raguwar garkuwa da mutane, amma har yanzu ’yan bindiga na bin mutane suna yi musu fashin dukiyoyinsu.

“Yanzu babbar damuwarsu ita ce yadda za su samu mai a baburansu. A makonnin baya, ina tuka babur a kauyenmu, gungun wasu ’yan bindga hudu suka tare ni suka tambaye ni ko ina da mai. Dole ta sa na sauya hanya

“Yanzu tare masu babura suke yi suna zuke musu man fetur, ba kamar da ba da suke garkuwa da mutum su nemi kudin fansa. Da watannin baya ne da garkuwa da ni za su yi,” inji Aliyu.

A lokacin hada wannan rahoto, wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, amma bai same shi ba.