✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Najeriya ce kasa ta 8 mafi hadari a duniya’

’Yan Najeriya na kokwanton cewa gwamnati za ta iya magance matsalar tsaro a yankin Arewa da ma kasar baki daya

Sarakunan Arewacin Najeriya sun bayyana damuwa cewa yanayin tsaron kasar ya kai ga ’yan kasar na kokwanton cewa gwamnati za ta iya magance matsalar da ke addabar yankin da ma kasar baki daya.

Shugaban Majalisar Sarakunan Arewacin Najeriya, Sarkin Gummi, Mai Shari’a Hassan Lawal Gummi, shi ne ya bayyana haka yana mai nuna takaicinsa kan yadda Najeriya ta shiga jerin kasashen mafiya hadari a duniya, irin su Afghanistan da Syria.

Sarkin Gummi ya ce, “Yanzu kasarmu ta yi kaurin suna wajen ayyukan ’yan bindiga da yin garkuwa da mutane — ita ce ta takwas a jerin kasashen da suka fi hadari a duniya, irins su Afghanistan, Syria, Iraki sa Somaliya.

“Yanzu a Najeriya har makarantu ake biana yin garkuwa da dalibai; Su kansu sarakuna da sauran masu sarautu ba su tsira ba, ana garkuwa da su domin karbar kudin fansa.”

Sarkin Gummi ya bayyana haka ne a wani zama da majalisar ta shirya ta kuma gudanar da nufin lalubo mafita ga matsalar rashin tsaro a Najeriya, musamman yankin Arewa, ta hanyar hadin gwiwa.

A cewarsa,  “Abin da ke faruwa a kasar nan na da ban mamaki; Idan aka yi la’akari da makudan kudade da matakan da gwamnati ke dauka a matakai daban-daban wajen yaki da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro; Sai Mutum ya ce to me ya hana har yanzu al’amura ba su daidaita ba?”

Taron na neman mafita daga matsalar tsaro, wanda ya gayyato masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a yankin Arewacin Najeriya ya samu halarcin sarakuna daga jihohi 19 na yankin.

Mai Shari’a Hassan Gummi ya ja hankalin mahalarta taron cewa tun daga lokacin yakin basasa Najeriya take fama da matsalar tsaro da suka hada da fashi da makami, rikicin kabilanci da na addini, satar mutane da sauransu.

Sarakuna na yin iya kokarinsu

Da yake jawabi a taron, Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bukaci sarakuna da masu ruwa da tsakin da kada su gajiya wajen lalubo hanyoyin da a aikace za su magance matsalar tsaron da ke addabar yankin Arewa da ma Najeriya.

Ya shaida wa taron cewa, “Za mu ci gaba da kokarin da muke yi a matsayinmu na sarakuna; Wadannan matsalolin ba za su kau ba, muddin ba a aiwatar da hanyoyin magance su da aka gano ba.”

Sarkin Musulumi, wanda shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, ya kuma bayyana wa taron masu ruwa da tsakin cewa sarakuna suna aiki ka’in-da-na’in wajen ganin an kawo karshen ayyukan ta’addanci.

Sarakuna sun kosa a samu zaman lafiya —Lalong

Da yake nasa jawabin a wurin taron, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya, Gwamna Simon Bako Lalong na Jihar Filato, ya jinjina wa sarakunan Arewa bisa namijin kokari da hangen nesansu wajen nemo mafita ga matsalolin da ke ci wa yankin tuwo a kwarya.

“Wanna taron ya nuna irin kishin da sarakunanmu ke da shi na ganin an samu zaman lafiya a kasar nan,” inji Gwamna Lalong, yana mai cewa matsalar tsaron ta hana kowa samun kwanciyar hankali.

Ya bayyana cewa taron ya nuna muhimmancin da ke akwai wajen samun hadin gwiwa tsakanin gwamnati da al’ummar kasa da hukumomin tsaro da kuma sarakuna wajen lalubo bakin zaren da kuma magance matsalolin tsaro a kasa.

Daga karshe taron ya kafa kwamitin mutum biyar da za su yi nazari kan wuraren da ake da matsaloli a bangaren tsaro, sannan ya gabatar da rahotonsa da za a aiwatar da shi domin magance matsalar.

Taron ya ba wa kwamitin mutum biyar din wa’adin kwana biyar ya gabatar da rahotonsa.